Wasannin ilimi.

Game da tambayar magajin garin Dankatsari da kuma samun taimakon na kungiya mai suna Secours Populaire, makarantar kananan yara wacce ita kadai ce a Dankatsari ta samu taimakon kayayyakin wasannin gwada ilimi a farkon shekara ta 2017.

Bencina.

Daliban makarantar Primary na makarantu uku na Cesson, da aka gayyato a watan Nuwamba shekara ta 2016 a matsayin wani ɓangare na Relais Solidaire don taimaka wa Dankatsari sun tattara kudi kusan euro 3,000 wannan zai sa a sayi bencina 20 don kowace makaranta uku na Dankatsari, har da aji na biyar na primary a makarantar da ke tsakar garin Dankatsari wanda take musayar ra’ayi tare da aji na biyar na ‘yan primary a makarantar Burgchevreuil da kuma makarantun Bawada Dagi Sanke da Mullela.

‘Yan Aji uku na dalibai masu shekara biyu a kwalejin Cesson sun tattara kudade wannan ya ba da damar sayen bencina bakwai don makarantar primary ta Lugu.

An ba makarantun tsakiyar Dankatsari, Bawada Dagi Sanke, Mullela da Lugu teburori masu kujeru a watan Yuni 2017.

A shekarar 2020, an gyara benci guda ɗari da goma sha biyu a Kwalejin Dankatsari albarkacin gudummawar da aka tattara a lokacin Relais Solidaire na makarantun Dankatsari, tare da halartar ɗalibai 800 na makarantun firamare uku na Cesson-Sevigne.