An kammala wannan mataki.

Maganar kafawarshi

Bayan da gwamnati ta fara maido hankali wajen al’amurran garin lugu ne aka kafa ɗakin maganin, dangance da wata hulɗa da ta shiga tsakanin Tarbiyya Tatali da garin. Mutanen garin sun tara jikka 171 da gwamnati ta tambaya domin ɗakin shan maganin ya kama aiki sosai da sosai, ta hanyar sayo magungunna. Al’ummar garin Lugu ta yarda da lafiya ke gaban komi, duk da gaskiyar da ta ba al’adunta na azna. Da haka ne ayyukan kiwon lafiya suka fara gudanar tare da wani malamin likitar da al’ummar ta zaɓa, kuma gwamnati take biya.

Dangance da bin ayyuka sau-da ƙafa

Tarbiyya Tatali tana ziyartar ɗakin maganin kai-da-kai. Kuma a cikin lokaci 2 an samu magungunna na jikka 100.
Sai dai, a shekara ta 2006, an yi lura cewa malamin likitar yana nuna sanyin jiki ga aikin, kuma ayyukan ɗakin maganin ba su tafiya yadda ya kamata. A lokacin nan aka samo wani wanda ya fi ƙwazo da himma ; sai Tarbiyya Tatali ta riƙa ba shi wani tukwici a kowane wata, har tsawon shekara 1 saboda himmar da yake nunawa.

Femmes de Lougou