Dabarun samun ruwa cikin karkarar Dan Katsari duka
An ci gaba da wannan aiki dai tare da samun [haɗin gwiwar Cesson Dan Katsari], Taimokon kuɗi na Cesson a sunan Udin-Santini da kuma taimakon wasu ƙawayanta (ƙasar Nijar, Ma’aikata mai kula da harakokin wajen ta Faransa, ofishi mai kula da ruwa ta Loire Bretagne, ƙungiyar cakuɗe mai samar da ruwan tsabta ta Renne.
Shi ne
- A 2011 gyaran wurin ruwan tsabta na Dogontapki (wani gari a gundumar Dankassari)
- A 2013, samun kayan aikin ruwa don garin tahirin Lugu (fadar ruwa da wurin pampon biyu)
- Domin [Shirin na’ura mai aiki da karfin ruwa>65], yin nazarin illahirin busatun ruwa na kauyuyukan Dankastari da kuma gyara wani shirin horo.
Ƙarshen shekarar 2013, wurin ruwa uku aka gyara a Karki Mallam, Dan Keda da Marake Tudu. A shekarar 2014, an gyara wurin samun ruwa 3 a Jarkasa, Kawadata, da Bawada Daji.
Farkon shekarar 2014, wani tsari na horo ya shafi 55 COGES na mutane 5, a cikin su akwai mace 2 ko da yaushe. Wurin horon na kwana 4 an gabarta takardun da ake aiki da su, da yadda ake anfanin kula da wuraren samu ruwa, da kayayakin aiki, an samu tautanawa da ‘yan sa hannun maza da mata.
A watan juni 2015, an yi horon gungu biyar na ‘yan gari ko wane na da mutane 22, an ba kowane gari leda 2 na kayan aiki, inda aka ba CPGES horo.
A shekarar 2015, ana cikin yin wata karamar AEP ta garuruwa a Bawada Gida. An sake karamin Tankin AEP na Dankatsari an samu babba, kuma za a kafa wurin samun tsarkakun ruwan sha cikin sababbin unguwoyi. An gyara karamar AEP ta Dogontapki, ‘yan gari sun huta da shan ruwa tafki maras tsarki.
A shekara ta 2016, rijiyoyi shida aka gyara a cikin kauyuka na Marake Rogo, Guizara, Sitrate Adarawa, Chanono Dan Tudu, Tsaba Abula, yawan mutanensu sun fi mutane 3000.
Tsarin shirin horo na COGES ya ci gaba har karshen shekara ta 2016 tare da sabin COGES 30 wato kamar rukunoni 5 masu mutane 30 kowane. Har ila yau an yi horon masu gyare-gyare. Rukukoni uku na mutane 20 kowane aka yi wa horo, an ba kowane gari akwatin 2 na kayan aiki in da aka yi horon COGES a farkon shekara ta 2017.
Rijiyoyin bakwai aka gyara a cikin kauyuka na Tunzurawa, Kolmey-Fulani, Korongomey, Muléla, Goni, Goho da Karki-Fulani a farkon shekara ta 2017. An fara ayyukan ran 24 ga watan Maris.
A wani ɓangare na shirin “samun ci gaba da manufofin raya kasa a kauyuka na Dankatsari”, gyare-gyare wuri goma na samun ruwa (a garuruwan Gugui, Saran Allah, Kore Djibo, Fareye, Tudu Bare Bari, Kujak, Kassaura, Gobro (Kumchi), El Gueza da Chinguila) an yi kuma gyare gyaren rijiyoyi bakwai (a garuruwan Garin Mai Yodo, Kaura Lahama, Dadin Kowa, Korongomey na fulani, Kadandame, Kolmay da Bourtou ). An yi kuma horon kimanin mutane 170, da masu ajiyar kudi 85, da kafa wani shirin na AEP da kuma rijiyoyi uku.
Shekarar 2019 - 2020: a matsayin wani ɓangare na shirin “Ci gaba mai ɗorewa a Dankatsari” gyaran tsubirin rijiyoyi goma sha biyu (a ƙauyukan Garin Dan Zomo, Yazuzu, Zauren Zumo, Gulmuni, Sabon Gari Zunurma, Gannas, Kolmey, Angoal Kassa, Tani, Montangarey, Dunhuimawa da Garin Maude) da kuma gyaran rijiyoyi goma sha biyu (a ƙauyukan Kamrey Kore, Mailo, Duzu, Gubey Koakore, Kumtchi, Nakigaza Dechi, Huda Massari, Tsaba Sabua Rigia, Kukoki Gaya, Kore Gabas, Yassedji da Kalgo Zunzurma) kuma da kafa karamin wurin samun ruwa na ƙauyuka da yawa a Kadandame.
Gine-gine ko gyaran wuraren ruwa sun sa yin horo ga mazaunan ƙauyukan da abin ya shafa domin tabbatar da cin gashin kansu ta fuskar kulawa da abubuwan da aka kafa musu.
A shekarar 2022- 2023: Kafa karamin pompo a Goho da tashar ruwa mai zaman kanta a Gulbi, haƙin sabbin rijiyoyi uku a Tunzurawa Gwada Guné, Dan Zaure Peulh da Rukutu, tare da tallafin AELB da CEBR. Jihar Nijar na bayar da gudunmuwar da karamin pompo guda biyu, daya a Lilato daya kuma a Bawada Dagi.