An kammala wannan mataki.
Raƙumin daji fari na Nijar, da aka ceto daga karewa
Raƙumin daji fari na Nijar da ake kira (Giraffa camelopardalis peralta) wani irin raƙumi ne mai zane da haske.
Yawansu dai wajen 50 ne a skekarar 1996, a 2012 sun kai 366. Cikin matsaloli akwai farin da yanke yankan itatuwan da yake ci, da sauyawar jeji ya koma gonakin hatsi da farautar da ba ta dace ba, «‘ƙaton daji » ai ko da ya ɓata sam sam.
Ayyukan ASGN (ƙungiyar ceton raƙuman dajin Niger) da jawo hankalin ƙasar Nijar, sun sa ya ceto yawan raƙuman dajin Nijar daga ɓacewa.
Garken raƙuman dajin Nijar suna kudu masa yamma da Nijar cikin jihar Dosso a Kure. Raƙuman dajin suna zuwa kusan ƙauyuka Dankatsari neman abinci, a kilometer 200 da Kure, musamman ma lokacin girbin wake, abinda suke so sosai. Tilas a ja-goran su zuwa arewa don su daina ƙetara iyaka zuwa Najeriya, idan ake farautar da ba ta dace ba.
Don ceton raƙuman daji, ya kamata a taimaki jama’ar wurin
Bisa wannan ne, garken raƙuman dajin Nijar ya samu shiga wani tasri na ceton da tatalin kera ayyukan a zo a gani.
Jama’ar Nijar ta nuna jin da’dinta game da wannan farin raƙumin daji. A yanzu dai tana matasyin gadon ƙasa.
Tasrin raƙuman daji sakakku, daga Nijar zuwa Cesson-Sevigne
Farkon 2014, Jean-Pierre Estournet da Abdul Aziz Sumaila sun je Rahoto Nijar sun ɗauki hotunan (hoto da video) na raƙuman daji na Kure.
Daga 19 ga watan mayu 2014, a Cesson Sevigne, tasrin « Raƙuman daji sakakku » zai shafi bangarori dayawa.
- A zo a gani : Daga 26 ga watan mayu zuwa farkon watan jully : hotunan raƙuman daji sakakku a waje (Square Jean Bucher). Daga 19 ga watan mayu zuwa 6 ga watan juny : Nunin a zo a gani a Espace Citoyen, kuma da hotuna hudu masu nuna aikin ASGN.
- Fim : wani fim mai tsayon minti 10 da wata gabatarwa ta minti 8 na aikin Bioparc na Doue na Fontaine don raƙuman dajin Nijar, za a yi su a wurin mai suna Espace Citoyen.
- Taron : ran 27 ga watan mayu, a wurin kimiyya na Rennes, game da saduwar da ake kira Talattar kimiyya. Masu taron : Pierre Gay, daraktan Bioparc na Doue na Fontaine da Jacques Rigoulet, mai kula da lafiyar dabbobi, a jahar Jardin botaniques et zoologique, a gidan kallo mai suna gidan kallo na tarihin halicce-halicce.
- Wasanni : ran 27 ga watan mayu saduwa a Cesson da mai yin dabbobin na icce Omar Sekou dan Nijar. Zai yi raƙumin daji don nuna wa jama’a da kuma saduwa da Pierre Gay da zai ba da bayani a kan yadda za a gane ra’kuman daji da rigunarsu.
- Jarabawa na yan makaranta : Tambayoyyi, idan an ci nasara za a samu raƙuman daji na icce ko na jan ko farin karfe.
Garin Cesson-Sévigne, AESCD, wurin kimiyya, Bioparc de Doué na Fontaine, ASGN