A Yammacin Afirka, a birni da kuma a karkara, mata suke kullawa da samun ruwa na rayuwar yau da kullun na iyali: sha, dafa abinci, wanka, wanki. Miliyoyin mata ko ’yan mata, ba su da ruwa a gida ko ma a cikin daki. Dole ne su yi tafiya na ’yan mita ɗari, wani lokacin ’yan kilomita, da abin daukar ruwa wanda, da zarar an cika, yawanci za su ɗauka a kawunansu. Duk da waɗannan matsalolin, wuraren samun ruwa kamar, rijiyoyin burtsatse, da tafkuna sune wuraren rayuwa da zamantakewa, taimakon juna da mu’amala mai daɗi idan suka ganu.

A Abiru Kwas

Kashi na farko na baje kolin shi ne sakamakon ayyukan filaye da aka gudanar a lokacin bazara na shekarar 2024 a kasar Abiru Kwas, a matsayin wani bangare na nazarin zamantakewa. Gagnoa, dake tsakiyar yammacin Abiru Kwas, yana fuskantar ƙaƙƙarfan ƙauyuka, wanda ke nuna bullar sabbin unguwanni. Wannan shi ne lamarin unguwar “marasa doka” inda, in ban da wutar lantarki, mazauna yankin ba su da sauran ayyukan yau da kullun har ma ruwa. A hotuna, za mu iya ganin shigarwa tare da rijiyar burtsatse da aka haɗa da famfo inda ake samun ruwa kyauta. Hakanan ana iya amfani da ruwa don yin abubuwan sha da sayar da su. A ƙauyen Demidugu , kimanin kilomita goma daga Gagnoa, dole ne a je rijiya don samun ruwa.

A Nijar

A samu Kashi na biyu ne daga aikin kwararrun masu daukar hoto guda biyu a Nijar da Faransa don nuna irin ayyukan da kungiyar Tarbiyya Tatali ta gudanar, AECIN tana cikin su. A Dogondutsi, a wata unguwa ko kuma a ƙauyen Lugu, mata ne ke kullawa da batun ruwa, kuma ruwan ba a samun shi kyauta. Don yin wanki, ana amfani da tafkuna sau da yawa. Samun ruwa don haka ya kasance abin fifiko a yankunan karkara. Taimakon Hukumar Ruwa ta Loire Bretagne da Rennais Bassin mai hulawa da samun ruwa a Nijar ya ƙare tare da juyin mulkin Yuli 2023.

Gabatar da nunin

An kirkiro nunin ne don Village des Sciences kuma an nuna shi a Champs Libres a Rennes daga ranar 4 zuwa 6 ga Oktoba, 2024. A ranar Juma’a 4, za mu samun ziyarar ƙungiyoyin makarantu tara, Asabar 5 da Lahadi 6 za a sadaukar da duk jama’a kowa da kowa.

Aikin ɓangarorin da ke samun goyon bayan Collège Doctoral de Bretagne kuma Jami’ar Mission Égalité ta Rennes da Ƙungiyar Musanya Al’adu ta Niger (AECIN) ta Ille-et-Vilaine ta haɓaka.

Bayanin hotuna:
- A Abiru Kwas : a Gagnoa rijiya da famfo 1-3, abin dauka 4, saydawa 5, a Demidugu rijiya 6, Photos daga Abdul-Aziz Dembéle .

  • A Nijar: a Dogonduci pampo 7-9, a Lugu pampo 10-11, wanki a tafkin 12, Hotunan Abdul Aziz Sumaïla da Jean-Pierre Estournet .