Unguwa ce a Kewayen Yamai inda yaran talakkawa da yawa masu fama da talauci ba su samu shiga makarantar boko ba. A nan ne wani ‘’huroje’’ da ya fara aiki a shekarar 2002 yake tara waɗanga yara ta hanyar wata ƙungiyar matan unguwar, sai ya ba su horon shekara guda don su samu shiga cikin sauran makarantun gwamnati a shekara mai zuwa.
Makarantar « fata » ta tsaida ayyukanta tsakanin 2013 da 2016.
Mahamadou saïdou aji tun 2017
An sake kafa sabon aji a watan Oktoba 2017. Akwai ƴan makaranta 31, ƴan mata 19 da ƴan maza 12, an samu damar yin wannan aiki da kudaden da AECIN ke biya. Makarantar yanzu dai a sa mata sunan Mahamadu Saidu, wanda ya kafa ta. Mai gudanar da ayyukan ta nuna da cewa inda ana son a yaki rishin zuwa makaranta na yara, to sai an kafa tsarin cin abinci a makarantar da rana. Saboda haka AECIN ta tara kuɗi yin starin.
A shekara ta 2018-2019, an koma makaranta ran 1 ga watan oktoba, ɗalibai 30 ke akwai, ’yan mata 8 da ‘yan maza 22. ’yan mata ba su da yawa saboda ƙanana ne, shekarunsu ba su isa su shiga makarantar unguwa ba. An yi wani annoba ta ƙarimbau a watan Janairu 2019, ta kama mai gudanar da ayyukan makarantar, amma yanzu kome na zuwa daidai. Lokaci ne mafi wuya a shekara don yanayi, kuma farashin abinci yana hawa. Hakanan an kawo ruwa kusa da aji wanda zai ba da izinin noman lambun a cikin makarantar.
An rufe ajin wani lokaci a shekarar 2020 saboda takurawar da aka sanya don shawo kan cutar COVID. An fara karatu na shekarar 2020/2021 a ranar 12 ga watan Oktoba, 2020. Rukunin daliban ya hada da ‘yan mata 15 tare da maza 15 wadanda aka zaba cikin dalibai hamsin. A lokacin bazara na 2021, ’yan mata goma sha huɗu da maza goma suka samu shiga aji na 4 na firmare, sauran ɗalibai shida sun samu shiga aji na biyu ko na uku na firmare.
A watan Oktoban 2021, ajin Mahamadu Saidu ya bude kofofinsa ƙumshe da dalibai 24 da suka hada da mata 7 da maza 17, a gundumar Tallague ta Yamai, za a kara yawan adadin yara mata ya zama ɗaya da na maza. Ajin a wannan shekara an sanya masa fitulun hasken rana guda 40. Wannan yana bawa ɗalibai da iyalansu damar samun tushen haske.
A cikin Oktoba 2022, ɗalibai 30 (maza 15 da mata 15) suka shiga makarantar. Kyakkyawan yanayin koyarwa ya sa ɗalibai 27 cikin 30 sun sake shiga tsarin karatun makaranta na yau da kullun a ajujukan CP, CE1 ko CE2.
A cikin 2023-2024 AECIN ta tallafa masa daga kudadensa: haɓaka wurare, kayayyaki makaranta, albashin malama, bai wa yara abinci a lokacin bazara, game da kudadan taron jama’a da aka ƙaddamar a ƙarshen 2023. Duba nan.
Ya yi aiki da ɗalibai 30 ciki ’yan mata 15 da maza 15 waɗanda ake ba abincin kowace rana ta aiki a bazara. Kowace rana da yamma almajirai suna komawa gida da fitilar hasken rana wanda zai ba su damar yin bitar darussa. A karshen shekarar makaranta, dalibai ashirin da takwas ne suka je yin jarabawa. Almajirai biyu ba su yi jarabawar ba saboda sun bar makaranta a ƙarshen zango na biyu saboda uwayansu su ƙaura. Bisa 10 an samu sakamako 9.71 zuwa 4.54 Daga cikin ɗalibai 28, mata 10 da maza 10 sun samu damar ci gaba zuwa CE2.

