Fa’idodin wasannin motsa jiki ba su da iyaka: ilmantarwa na demokraɗiyya yana sa musayarwa, girmama doka, neman ƙwarewa da karɓar kaye.

Kungiyar Matasan Nijar

Wannan shi ne dalilin da ya sa jihar Nijar, tare da goyon bayan sabis na Hadin gwiwa na Ofishin Jakadancin Faransa,yin wata, “Kungiyar Matasan Nijar
” (OJEN), da nufin farfado da ilimin motsa jiki da wasanni (EPS) ) tun makarantar firamare.
Aikin yana ta’allaka akan tsarin sadarwar illimi da al’adun gargajiya na Faransa-Nijar, tare da CCFNs na Yamai da Zinder, ofishoshin Faransa na Agadez da Maradi, da Lycée La Fontaine ta Faransa a Yamai.

OJEN ta kafa ƙungiyoyin 4 na ayyukan yanki, kowannensu yana tattara kusan mutane goma a CCFN Jean Ruch a Yamai. Kuma sakataran ƙungiyar ke jagorinta;
Ka’idarsa: Tsara wasannin motsa jiki tsakanin mata da maza (tare da daidaita adadin tsakanin ’yan mata da samari ga dukkan lamuran) a tsawon shekarar 2019/2020, da kuma a rubu’in ƙarshe na 2020.
Yara 36,000 ne na makarantun firamare 60, da ke cikin garuruwa 4 (Yamai, Agadez, Maradi, Zinder) abun ya shafa.
An horar da malamai 400 ga motsin jiki kuma kowace makaranta da ta halarci horon ta samu kayan aiki na asali: kaya na yara, kayan gudu na malamai, ƙwallon ƙafa, rugby, volleyball, kayan wasan motsa jiki da langa-langa, da akwatin cike da
Magunguna iri iri.

Tarurrukan tsakanin yakuna

Wasannin Farko na motsin jikin da Al’adun Matasa sun gudana a Zinder daga 29 ga watan Fabrairu zuwa 1 ga watan Maris 2020, ɗalibai da yawa daga yankuna 4 suka haɗu.
Daga 23 zuwa 25 ga watan Oktoba shekarar 2020, Maradi ta shirya taron ta na tsaka-tsaki, tare da halartar ɗalibai 20 daga Maradi, ɗalibai 10 daga Tibiri da ɗalibai 10 daga Dogon Dutsi da Dankatsari a matsayin wani ɓangare na haɗin kai Orsay -Dogondutsi da Cesson-Dankatsari, wato ɗalibai 5 daga Dankatsari (maza uku da mata 2) da ɗalibai 5 daga Dogon Dutsi (’yan mata 3 maza biyu). Ba tare da kilgon ɗaliban da suka zo daga sauran yanki ba, wato mahalarta 100 gaba ɗaya. A kan shirye-shiryen abubuwan da suka faru: gudu, ƙwallon ƙafa da langa-langa, tare da yin zanga-zangar wasanni (wasan tsere - vortex - taekwondo - rugby - volleyball) da ayyukan al’adu.

Gasar Olympics na matasan Arewa

A cikin tsarin OJEN, an shirya “Kwallon kafa tsakanin makarantu da kuma Gasar Olympics”, wanda zai gudana a cikin kananan hukumomi biyu na Dogon Dutsi da Dankatsari, a zaman wani bangare na hadin gwiwar Orsay - Dogon Dutsi da Cesson-Dankatsari .

Kungiyar Kwallon Kafa ta Arewa, watau mambobi 9 na CA na Hukumar Gudanarwar AFC, da ’yan wasa 22 na kungiyar sashen, da masu horar da su mutum uku, da kuma malaman koyar da wasanni ke aiwata da kula da wadannan Olympiads. Suna samun taimakon kungiyar RAIL da RAEDD, tsarin Orsay - Dogon Dutsi da Cesson-Dankatsari, da kuma tarayyar gudanarwar COGES na makarantun firamare.
Har yau suna samun taimakon tallafin kuɗi na Ofishin Jakadancin Faransa, da na kungiyar Musanya da Dogon Dutsi.

A cikin ƙananan hukumomin biyu, ya shafi ‘yan aji na hudu da na biyar na makarantun firamare huɗu waɗanda suka nuna kuzari wajen shirya wasannin Olympics na ƙwallon ƙafa, da kwalejoji 18 na ‘yan aji na daya da na biyu, don tsara Gasar wasannin tsakanin ƙungiyoyi masu haɗaka a gauraye.

Gasar ta Olympics ana yin ta ne tsayon watanni 7, daga Oktoba 2020 zuwa Afrilu 2021. A watan Fabrairu 2021, Also Saïdu, shugaban AFC ya bude wasannin tare da yin koyo na farko.

Abdul Aziz Sumaïla mai daukar hoto dan Nijar ya yi rahoton daukar hoto, kungiyar AESCD ta dauki nauyin shi. An yi wannan baje kolin “Dogon Dutsi Dankatsari a tsakanin makarantun Olympics (Niger)” a farkon Yuni a Nijar a CCFN. An buga shi a shafin yanar gizon Tarbiyya Tatali.

Matasa goma da suka zo na farin daga gasar wasannin Olympics, na Dogondutchi da Dankatsari, aka gayyata zuwa Yamai a ranar 16 ga watan Yuni a matsayin wani bangare na ranar yara ta duniya.

Wasannin motsa jiki a makaranta

 
Tun daga firamare har zuwa sakandare, shirin wanda ’yan wasan Nijar da RAIL da RAEDD, ya ba da shawarar inganta fannonin wasanni kamar haka a Dogondutsi da Dankatsari:  

  • Wasannin motsa jiki ta hanyar juriya, gudu, da tsalle tsalle
  • Kokawa ta gargajiya
  • Kwallon kafa
  • Langa
  • Wasan kwallon raga 
  • Kwallon hannu
  • Rawar halitta da wahayi na gargajiya
  • Ballet 
    da kuma shirya horo don inganta iyawar masu ruwa da tsaki.

An gabatar da shi ga MEAE ta birnin Orsay tare da haɗin gwiwar Echanges Orsay Dutchi, an amince da aikin a lokacin rani na 2021 na tsayon shekarar 2021 zuwa 2023.

An bude taron a hukumance a ranar Litinin 19 ga watan Oktoba, 2021 a Dogonduchi gaban hakiman kananan hukumomin biyu da hukumomin makarantar. 

Sannan aka gudanar da horar da malaman motsa jiki 25 na sakandire wato EPS wadanda za su taimaka wa malaman makaranta 65 kowane mako a duk tsawon lokacin karatun don karfafa ayyukan wasanni a kwalejoji.   

A ranar 29 ga Janairu, 2022, an gudanar da bikin wasannin motsa jiki a Dogondutsi, daliban Dankatsari sun zo cikin bas don halartar wasannin.