Idi Nuhu ya ziyarci Saint- Brieuc a watan Nuwamba 2015 a lokacin watsa fim ɗinsa na Tarihin da aka zana zuwa ga talakkaya mai wallafa ayyukan AlbulKarim Nasaua, ɗan zane-zanen Nijar ne a cikin Watan Doc . “A Nijar , wasan zane-zane na da amfani a wani lokacin don kyautata zama jama’a. Ta hanyar fasali na wani matasa na Nijar Abdulkarim Nasaua da zane-zanensa da ake samu cikin unguwannin, Darekta Idi Nuhu yana kawo taimakonsa game da wasanni masu nuna hallin rayuwar siyasa cikin kasarsa .”

Ya rubuta wani wasa na rufe ayyukan wasanni na “Maradi Kolliya”, ta 2015 da aka yi bana a Maradi, wasan da ake yi na samun yancin kai a kowace shekara.

Fimmomin Idi Nuhu (kamar darektan ko marubuci)

 • Daraktan fim ’Yan mata uku a Dankatsari, minti 15 shekara ta 2018.
 • Wallafa fim Ruwa falala a Lugu, 13 m, 2016.
 • Yin fim mai suna Tarihin zane don tallakawa, minti 52, shekarar 2012.
 •  Fim mai suna Rana ɗaya tare da Alhuseini, minti 13, shekarar 2011.
 •  Fim mai suna Bayan wasa (minti 40), bisa wasan Cure salée ko gishirin Cure - Ingall, shekarar 2010.
 • Daukar murya na fina-finai, a cikin tsarin Hasken Nijar, na Forum Afirka na Yamai, 2009-2010.
 • Réalisation de Quête ..., fim na makaranta a St. Louis a shekarar 2009
 • Haɗin kai, wasan gidan talabijin kashi 52 ne na gidan fim ɗin Mali (CNCM) (sa hannu a rubutunsa).
 • Cida da gobara, wasan kwaikwayo a rediyo da Zarbarmanci da Hausa a kan haihuwa da kiwon lafiya wajen matasa (sa hannu a rubutansa).
 • Lafi-Keneya-Lafiya, wasan kwaikwayo a rediyo kashi 15 ne ya shafi Burkina Faso, Mali da Nijar, samfurin yi tunanin a Burkina Faso (sa hannu a rubutansa).
 • Gobe ​​da haske, fim mai kashi 144 don al’ummar rediyo, da son matasa da kuma jama’a Media Center, USAID ta ba da taimakon kuɗin wannan aikin, da kuma watsa shirye-shirye ta hanyar tauraron ɗan Adam a Afrika ta Yamma da kuma a kan muryar Sahel (sa hannu a rubutunsa).

Ayyukan wasan kwaikwayo ( rubuce-rubuce da kuma shiryawarsu )

 • Biya mai abu biyu, wanda aka yi daga Afirka mai shawa na Bubu Hama. Yan wasan nan masu suna les tréteaux du Niger suka ƙerkero shi ran 21 ga watan aprilu 2006 a CCFN ta Yamai.
 • Ruwan Zuma wanda aka ƙera a Agadas lokacin haɗuwar wasannin kwaikwayon Nijar Editan 2003. An watsa wannan shirin a kan talabijin a watan Satumba shekara ta 2004.
 • Gambara - sul , rubuce-rubuce da kuma shiryawa , Yan wasan nan masu suna les tréteaux suka ƙera shi lokacin, haɗuwar wasannin kwaikwayo na Nijar Edita na 2003 .
 • Badadrum ko matsalolin Sakarai , wasan da aka ƙera ran 27 ga watan Yuni , 2002 a Ouagadougou (Burkina Faso ) lokacin RECRÄTRALES Edita na 1. An sake wallafa rubutu cikin wani sabon shiri na Cheick Kotondi , a wasan ganuwar ‘yan- Afirka na Algerias a watan Yuli 2009 , da kuma wurin wasan Black Arts a Dakar a shekara ta 2010 .