Maganin tamowa ‘’Spirilin’’
Wani tsiro ne da ke fitowa bakin tabkuna a ƙasashe masu yanayi mai zafi. Ana iya shuka shi cikin guraben ruwa kuma ya fito sosai. Sai tsiron ‘’spirilin’’ ya bushe ne ake yin amfani da shi. Ya ƙumshi sinadari iri-iri na gina jiki, da kariyar jiki. Garam 1 zuwa 2 na wannan tsiron a kowace rana, ya isa warkar da yaron da ke da tamowa a cikin sati 5 zuwa 6.
Hulɗa tsakanin ƙungiyar ‘’Antenna Technologics’’ da Tarbiyya Tatali
Antenna Technologic, ƙungiya ce mai gurin yaƙi da tamowa. Ta ɗauki niyyar bunƙasa shibkar tsiron ‘’spirilin’’ a cikin ƙasashe masu tasowa. Tarbiyya Tatali ta amince ta ƙulla hulɗa da wanga tsarin. Tarbiyya Tatali ta ɗauki niyar ba da spiruline abinda ya kai kashi 20 cikin ɗari daga kalarta don taimako zuwa ga masu tamowa.
Gina guraben ruwa da noman tsiron
An zaɓo wurin yin guraben ruwan, an sanya wutar lantarki da pampo, an yi guraben, da magewaya, da ɗakuna, kuma an shibka tsiron cikin guraben.Akwai mutumen da ke motsa guraben a kowace awa, kuma kowace rana. An shibka ‘’spirilin’’ a farkon lokacin zafi na shekara ta 2007, kuma aka fara ɗibar shi. Malaman da ke yi wa yara masu tamowa magani a Dogon Dutsi, sun yarda da ingancin tsiron ‘’spirilin’’; yana gaggauta warkewar yaran da aka riƙe a lilita ; a Nijar yara masu ɗimbin yawa ne suke da tamowa.
Halin da ake ciki a shekarun 2014-2016
A yanzu dai babu bashi albashin. An samu hanya ta saida maganin tamowa akan farashi mai rahusa cikin ɗakunan shan magani na garuruwan. Wannan dai game da taimakon kuɗin AECIN.
Yanayin a shekarar 2017-2018
Ƙaddamar da Antenna Technologie Nijar ta kara inganta kasuwancin wannan maganin tamowar a Niamey. Hanyoyin farashin-tallafin kuɗi ya takaita. An sake fara yin Kyautar agaji a asibitin Dogon Dutsi. A karshe, an yi aikin gyare gyaran gonar da kayan aikin lantarki na makamashin rana tare da kudade daga Kamfanin ruwa na Nijar. Bidiyo.
Yanayi a cikin 2020
Kodayake yanzu ba ta ba da gudummawa don tallafawa gonar spirulina, AECIN na ci gaba da lura da wannan aikin ta hanyar rahoton gonar na kowane wata. An samu kilogiram 156 a shekarar 2020 (idan aka kwatanta da kg 328 a shekarar 2019). Daga cikin kilogiram 46 aka kaiwa asibitin Dogon Dutsi kuma an ba da kilogiram 45 zuwa wata cibiyar abinci mai gina jiki a Yamai da kuma wata kungiya mai zaman kanta a Zinder. Za’a tabbatar da makomar gonar spirulina tare da wadatar da kantuna na dindindin.
Tsayawar ayyukan a 2021
Ba a sami mafita ta dindindin na tattalin arziki ba, gonar ta dakatar da ayyukanta a cikin 2021.