Wannan aiki na pangaren likita bai samu ‘bunkasa sosai ba a Nijer. Mahimman likitoti ko « hôpital » na ƙasa dai ne ke da wannan ma’aikata, sun tashi kimanin ma’aikata 10. amma akwai wata makaranta da ake iya koyon wannan aiki inda ake tsamanin ‘dalibai 58 za su samun digri a shekarar 2013.

Wannan shirin yakan taimaka ma masu rishin galihu domin yi musu aiki.

Mafarin kffa projen

Sabrina, Sandra da Camille sun samu yin aiki a baban likitan Yamai a shekarar 2008. nan ne suka yi aikin taimako zuwa ga marasa galihu. Nan ne suka gane cewa, da wurin ma’aikatar ba ta da abubuwa datatu don gudanar da wannan aiki. Don haka ne suka kotamta ma shi gabaninsu da ya kamata a duba a gani. To kambacin wannan ne aka kafa wannan projen ko shirin.

Gurin projen

Babban gurin shi ne na yi wa masa rashin lafiya magani cikin dakunan da suka dace.

 Masu aikin gyaran juyoji hudu ‘yan Nijar aka yi tun watan Disamba 2009. Mahamadou Diadié, sa’an nan Maman Sani, sai Kadjidja tun watan Maris 2017.

Raskonar shekarar 2009-2010

Domin haka ne aka ‘dauki wani kwararen ma’aikaci a wannan pannin a shekarar 2009. Ma’aikatan wannan pannin na Faransa sukan taimaka wa zuwa ga kulawa ga marasa lahiya ko horo zuwa ga abukan aikinsu.

Daga oktoba na shekarar 2010 zuwa janury na shekarar 2011, ma’aikatan Faransa suke kokarin ba da karatu ko horo kowace juma’a da yamma.

 Tun watan Janairu 2011, ƙungiyar take da dan Nijar mai aikin gyaran juyoji tun da an dakatar da Zaman cuɗayyar juna na ‘yan Faransa saboda rahin kwanciyar hankali.

Raskonar shekarar 2011-2012

Adadin waɗanda suka yi ziyara a shekara ta 2011 ba ya dayawa, sakamakon kamawa da kashewar Antoine da Vincent ranar 8 ga watan janairu a Yamai. A yanzu dai babu maganar ziyara, saboda rashin issashen tsaro ga yan Faransa.

Game da sha’anin kuɗi na huroje, kuɗin da muke kashewa, dai shi ne na albashin Diadé. A watan september Nicolas wani dalibi a makarantar gyaran juyoji ya yi wata hidima ta « karya kumallo » wannan ya sa aka samu abin biyan albashin Diadé na wata Uku.

Albashin Diadé dai jika amshin ne ko wane wata (kamar euros 8o) wannan dai nauyi ne ga AECIN, amma muna shakka nan gaba ƙasar Nijar za ta ɗauki biyan albashin nan : kamar albashin na wanda ke bautar ƙasa, ko kuma shiri na neman zaman ma’aikacin kiwon lafiya na gwamnati .

Har yanzu ba a samu zuwa so da so ba
Dadié ya sake ma’aikata. Yanzu dai shi ke aikin bautar ƙasa a baban likitan Yamai. Muna fatar za a ɗauke shi aiki bayan aikin bautar ƙasa domin taimaka ma marasa galihu.

Diadie

Malam Diadié ya sake ma’aikata kuma ya fara aikin bauta ma kasa a cikin baba laptani ko babba asibitin Yamai zuwa tsawon shekara biyu tun alip dubu biyu da goma sha biyu. Ya bar tsohuwar ma’aikatar kula da musakai a kambacin rauni ko rishin lafiyar jijiya da ake kira traumatologie-orthopédie da neurologie a faransance, inda ya koma sarushin tahi-yiya na laptani. Muna fatar Gomnatin Nijer za ta dawasa aikin ɗinɗin bayan ya kare aikin bautar ƙasa don samun ma’aikatan da suka dace a laptanin.

Raskonar shekarar 2013-2016

Wanda ya ɗauki wurinshi tun daya ga watan febrari na alip 2013 shi ne malam Maman Sani koraran ma’aikacin irin wannan aiki da ya samu diplomar sa a lakkol ɗin nan ta Yamai. Shikan tafiyar da aikin sa a wurare domin ci gaba da taimaka ma marasa galihu da taimaka musu da yi musu maganin ciwon dake damuwar su.

Maman Sani a sake yanayi kuma ya soma aikin bauta ma ƙasa a asibitin kambacin shekara biyu a 2013. Sai dai kuma ba kamar wadda Diade ya yi ne ba. Yakan tafiyar da aikin a cikin sharushin tabuwar kokkolwa, nakasa da na jijiya. Kada yakan samuwa, ya kan ci gaba da aikin sa a wurin da ya dace. Muna fatar gomnati zai dauke shi aiki kuma da nauyin albashinsa kadan ya kare aikin bautar ƙasa. Wannan shi ne kambacin gurin kungiyar don kula ma kowa da kowa a fanin nakasa.

Ƙasar Niger ko in ce gomnati zai daukin nauyin albashin dai dai lokaci. Mu kan tal’lahwa abinda ya kasa ga albashin domin kulawa da rahoto da kingin su domin samun labaru ko wane wata akan wannan gurin kowane lokaci

A wannan kishin kudi na wata, an kara wani a shekarar 2015 don sayan kayan aiki ( kekunan taimakon tafiya 2 , sandar tafiya biyu, da kuma wata irin sanda ita ma ta tafiya biyu) .

Ana samun damar yin hurojen aikin gyaran juyoji da kudin AECIN

Bugu da kari, dalibai hudu na makarantar aikin gyaran juyoji na Rennes, sun tuntuɓi AECIN don tsara ayyukan a Nijar a lokacin farko shekarar 2016.

Bayan aikin bauta wa kasa Maman Sani ya nemi ci gaba cikin aikinshi, shi ya sa ya bar aiki tare da mu.

RAEDD ta dauki a farkon shekarar 2017 wata sabuwar ma’aikaciyar gyaran juyoji, Kadija, don ci gaba da yin ayyukan a asibitin birnin Yamai.

Kadidiatu ta samu aikin a babban asibitin Yamey mai suna « hôpital général de référence » kenan ta tsayda aikinta a asibitin kwamun a karshen watan Maris. Ta ba da shawara a ɗauki wani likita mai gyaran juyoji don ya ci gaba da aikin da ta fara. Shi ne Gumar Abdul Aziz wanda ya fara aiki ranar 3 ga watan Mayu shekara ta 2019. Kamar dai Kadidiatu, ana biya shi da kuɗaɗen AECIN.

An dakatar da wannan matakin a cikin Maris 2020, saboda a samu damar yin wasu ayyuka da kudaden AECIN.

Salle commune, Hopital de Niamey


Hôpital Niamey DM par PromoChabrol

Video da Joanna ta yi a shekara 2010 lokacin da ta je zaman cuɗayyar juna
{{}}