An gudanar da horo kan rubuce-rubucen ayyuka daga ranar 5 zuwa 7 ga Mayu, 2023 a dakin taro na Dankatsari . Manufar horon shine koyon yadda ake rubuta ayyukan ci gaba, akan tsarin jigogi da aka gano ko kuma akan wasu da za a yi nan gaba.
 
Wannan horon da Nuvel Espoir ce ta yi shi da gudummuwar kuɗin AESCD tare da na Majalisar Garin Dankatsari (samar da ɗakin taro) da RAEDD (tallafawa ga sakatare na dindindin wadda ta zo daga Yamai)
 
Wakilan ma’aikatar kananan hukumomi Dankatsari da mambobin kungiyar RAEDD ne suka halarci horon .
 
Manufar ita ce rubuta takardun tsarin aiki.
 
Ayyukan da aka zaba sun kasance kamar haka

 • kafa sashen noman gandun daji
 • aiwatar da kayan kiwon shanu don samar da madara
 • hakawar wuri mai zurfi dona rika baiwa lambun kasuwar Marake Rogo ruwa
 • horar da mata akan yin sabulu da man shafawa don bambanta ayyukan samar da kudaden shiga
 • sayan sabbin amalanke don ungozamai
 • goyon bayan dandali kan ci gaban mutane da ayyuka karfafa al’adu
 • Samar da kayan aiki na zauren taro da dakin horo na majalisar garin
   
  An yaba aikin sosai, duk da haka taron bai yi tsayon ba shi ya sa ba a kai ga samun ayyuka masu nasara na gaske ba.
   
  Dole kenan a ci gaba da aikin.