An kammala wannan mataki.
Horon sabbin malaman
Domin samun shiga makaranta ga mafi yawan yara da shekarunsu suka isa, gwamnati, da ƙungiyoyi, da al’ummar garuruwa sukanɗauki sabbin malamai matasa waɗanda ba su samu horon koyarwa ba, ga kuma rishin albashin kirki.
Domin a sanya malaman hanya a farkon aikinsu, hurojen yake wallafa wasu takardu ɗauke da mahimman bayanai a fannin koyarwa don sulhunta masu aikin. An sa ran wallafa irin waɗannan takardun har 900. ƙwararrun malamai sun yi wasu takardun waɗanda mashawarta a fannin koyarwa tare da mambobin Tarbiyya Tatali (RAEDD) suka ƙaddamar bayan wani gwajinsu da hukumar ƙananan makarantu ta bi sau-da-ƙafa a cikin azuzuwa. Darussan da takardun suka ƙumsa za su amfani sabbin malamai wajen ƙwarewa ga aikin koyawar.
‘’GREFF’’ tana taimakawa ga horar da sabbin malamai ta hanyar larwan aikin a cikin azuzuwa, da shirya tarurrukan bayar da horo.