Horo a Dankatsari

Kungiyar ta RAEDD ta shirya wani horo na kwanaki 4 a Dankatsari a watan Yunin 2023, AESCD ta dauki nauyin shirin ta hanyar MEAE kuma ta yi shi ga mata 119 na kauyuka 10 na karamar hukumar Dankatsari da aka baiwa bashin kuɗi.
Manufar horarwar ita ce a taimaka wa mata su mallaki hanyoyin samar da ayyuka masu kawo masu kudaden ta yadda za su iya, karfafawa da/ko bambanta ayyukansu da na gamayya da kuma samun fa’ida daga gare su. Hanyar da aka yi amfani da ita don gabatarwa da haɓaka jigogi ita ce ta hada kowa, ta yadda za a sauƙaƙe fahimtar da gunguna hudu na mutane 30 kowanne. An danganta wannan ka’idar tare da nazarce-nazarce na musamman don taimakawa mahalarta taron su dunkule abubuwan da ya kamata a ba da fifiko a kan aiwatar da ayyukan samar da kudaden shiga. Sashen hidima na Dogonduchi na ma’aikatar bunkasa harkokin kariyar Mata da Yara, ne ya bayar da horon .

Ƙimar bashi

Cesson-Sévigne ta bukaci taron horon da gudanar da bincike kan wadanda suka samu ƙananan bashi kowace ta cika yar takarda. Binciken ya bayyana cewa samun kudin shiga, da farko kadan ne sosai (a matsakaita € 486 a kowace shekara), ya ƙaru fiye da 26% bayan bayar da ƙananan bashi. Matsakaicin shekarun wadannan mata shekara 45, suna da tsakanin shekaru 25 zuwa 75. Suna da ’ya’ya kamar 6 a matsakaici. Duk matan sun yi karatun yaki da jahilci, kuma 16 cikin 119 ne kawai suka je makaranta. Mayawacin su masu aure ne, amma 21 zawaru ne, 4 kuma suna dakin aure. A cikin matan aure, 46 su kadai ne a gidan ba su da kishiya (matsakaicin shekarunsu 35 ne ) kuma 48 suna da aƙalla kishiya guda (matsakaicin shekarunsu 50 ne). Hakan ya yi daidai da matsakaicin halin da ake ciki a Nijar inda aka yi kiyasin cewa kashi 50% na matan aure ne su kadai a gidansu wato ba su da kishiya. Samun wannan bashi ya ba da damar mafi yawansu (mata 78) yin ayyuka iri iri, musamman ta hanyar kiwo, amma suna ci gaba da ayyukansu na baya kamar yin masa, ko wani abu. Albarkacin samun bashi, wasu (mata 32) sun inganta yanayin ayyukansu na baya (kasuwanci, kiwo). Mata kadan ne (mata 9) ba su da aikin yi ko sai noman lokacin damina kawai, yanzu suka fara kiwo ko kananan sana’o’i. Sau da yawa ake iya baiwa gungunan mata ƙananan bashi yayin waadin biyan kuɗi ya kai. Za mu iya kimanta cewa tun daga 2017 ƙananan bashi da aka ware (1,306) ne kuma ya amfani kusan mata dayawa kimani 450.