Tamowa, matsala ce da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar Nijar. An kimanta kusan kashi 30 cikin 100 na yaran da suke fama da ita.

A lokacin matsalar abinci ta shekarar 2005

Daga shekara ta 2005 ne aka fara riƙe yaran da aka gano da tamowa mai tsanani a wani gidan likita na masamman da ƙungiyar ‘’Helen keller International (HKI) ta kafa. Yara 176 masu tamowa aka yi wa magani a wannan gidan likitar, tsakanin watan ogusta 2005 zuwa watan feburari 2006.

Tarbiyya Tatali ta yi lura da har mata uwayen yara, su ma suna da wannan matsalar ; kenan su ma sai an ɗauki nauyinsu. Mun sayi abincin kwana 45 na farko, kuma mun riƙa ba su sabuni 1 kowane sati. Daga baya sai ‘’Helen Keller Internationnal’’ ta ci gaba da haka.

Spirule maganin tamowa

Ya’dar da spiruline
Spiruline dai abu ce mai anfani akan yaƙi da tamowa zuwa ga yara matasa..akan iya cin gramme biyu zuwa biyar ko wacce rana ga kowane yaro. Amma ku’da’den da ake sawa a yi ta suna da yawa tunda sun tashi kimanin dala 18 000 ko a ce yuro 27 kilo gu’da kuma yan Nijer ba su saba ba da anfani da ita.

Tun kafa lambun spiruline, ake taimaka ma gidan likitan Dogonduci da 20% na spiruline.

Photo d’Alain Roux