Lugu yana fama da tsanantattar matsalar ruwa. A shekara ta 2002, pampon murtsatse 1 ke akwai ; sai yawan lalacewa, duk da yawan gyaran da ake yi mashi ; kuma rijiya guda ce mai zurfin metir 80, wadda mazamna garin da makiyaya suke yin amfani da ita ; ita ma tana yawan yashi. A wasu lokutta ma, ruwan tabki ne mutanen garin suke sha.
Wurin samun ruwa na Lugu
Garin Lugu ya samu ranar 12 ga watan fabrairu 2013, wurin samun ruwa na kanta.
A wurin dai akwai, wani ‘karamin shaton ruwa, da kankare, wato wurin ‘daukar ruwa mai pampo biyu, da pampo biyu da aka kafa, ‘daya cikin makarantar, ‘daya kuma cikin gidan lafiya.
An yi babban biki ranar 20 ga watan febrairu 2013. Parepe na Dogondutsi, da magajin garin Dankassari, da daraktan mai kula da sha’anin ruwa “hydraulique” na jihar Dosso, da na Dogondutsi, da wakilai hu’du na RAEDD, da mai ‘daukar hoto, da talabijin ta jihar, da sarakunan garurukan jihar, da wanda ya aikata aikin nan, da ‘yan garin Lugu, dukansu, suka taru bayan Sarauniya Aljima don muna murnarsu.
Fim [Ruwa falala Lugu->https://vimeo.com/268609761 yana nuna canji da samun ruwa ya kawo a cikin rayuwar garin.