An kammala wannan mataki.
A garin lillato, an ci gagarumar nasara ga jarrabawar shiga ‘’Kwaleji’’
Tsarin samar waKowane ɗan makaranta littafi na kowane fannin karatu, ya bada sakamako mai kyau tunda dukan ƴan makarantar Lillato su 51 na aji na 6, suka ci nasara ga jarrabawar shiga makarantar ‘’kwaleji’’a watan yuni na shekara ta 2002. Kafin wagga janabawar, babu ɗan makarantar garin da ya taɓa samun shiga ‘’kwaleji’’.Saboda wannan jin daɗin ne aka shirya wata gagarumar liyafa ta yabon ƴan makarantar da malamansu.
Akwai wata matsalar da ya kyautu a warware
Yaya shiga ‘’kwalejin’’ za ya kasancewa ? A cikin birnin Dogon Dutsi ne ‘’kwalejin’’ yake, mai nisan kilometir 30 da garin lillato. Kenan dole ne sai ƴan makarantar sun baro garinsu zuwa Dogon Dutsi. A yadda a saba gani, ƴan uwa da aminnan arzikin uwayen yaran ne suke karɓar baƙuncinsu a Dogon Dutsi har ƙarshen zamansu na ‘’kwalejin’’. Matsalar ita ce ta samun gidaje 51, kuma wani lokaci masu ƙarbar yaran suna sanya su wasu ayyuka daban don rage nauyin baƙuncin. Hakan yana haddasa gujewar ƴan makarantar daga ‘’kwalejin’’ tunda karatu ba ya haɗuwa da ayyukan gida ko na neman kuɗi.
Magance matsalar : ɗaukar nauyin abincinsu da wurin kwana
Domin magance matsalolin yaransu, sai mutanen garin lillato suka ɗaukar masu gidan hanya, suka sayi abinci da kayan dafuwar da ya kamata, kuma daga can aka kawo masu yi masu dahuwar da sauran ayyukan gida.
Sun nemi tallafi saboda biyan hayar gidan, kuma Tarbiyya Tatali ta samo masu shi daga kwamin ta ‘’Plénan le petit’’.
Tun shekara ta 2007 ne yaran suka fara shiga ‘’kwalejin’’ garin Gube da ya fi kusa da garinsu, kuma ba a tsinke tallafin kwamin ta ‘’Plénan le petit’’ ba ; ana yin amfani da kuɗin don sayo wa yaran lillato da suke ‘’Kwaleji’’ littattafai.