An kammala wannan mataki.
Tushen tsarin : hulɗa tsakanin côtes d’Amor da Nijar
Yau da kimanin shekaru 10 ne ƴan kokowar Nijar da na Bretagne suka yi saduwar farko a lokacin kasuwar baza-koli ta Saint Brienc da aka shirya albarkacin hulɗar da ke tsakaninCôtes d’Amor da Nijar, inda ƴan kokowar suka halarta. A nan ne aka samu cuɗayya tsakanin ƴan kokowar Bretagne da na Nijar ; sai dai cuɗayyar ba ta ɗore ba daga nan.
A wasannin ƙasashe masu aiki da harshen Faransanci na 2005 a Nijar
An farfaɗo da wannan hulɗar a lokacin wasannin na 2005, tunda akwai kokowa a cikin tsarin wasannin, inda ƙungiyar kokowar Faransa ta aiko ƴan kokowar Bretagne don ta wakilce ta. An yi nune-nunen fusa’o’in kokowa daga kowane ɓangare, hakan kuma ya ƙara danƙon amintaka tsakanin su. Hukumar ƙungiyar ƙasashen, da ƴan kokowar Faransa sun nuna gamsuwarsu da irin salon kokowar Nijar, kuma ƙasar ta Nijar ta yi farin cikin haka ; har aka fitar da wani littafi na mahimmanhotunan wasannin.
Ɗaɗin da mutanen Bretagne suka ji a wannan haɗuwar, shi ya sa ƙungiyar ƴan kokowar ‘’Gouren’’ ta yi ƙoƙarin gayyatar ƴan kokowar Nijar don su halarci wani zaman horon ƴan kokowa na ƙasa da ƙasa a ‘’Carhaix,’’ cikin shekara ta 2007, kuma da wata kwamɓalar kokowar gargajiyar ƙasar ‘’Ekos’’, tsakanin ƙasashe.