An kammala wannan mataki.

A albarkacin satin da aka keɓe a shekarar 2007 na nuna taimakon juna tsakanin kasashen, haɗin kan ƙungiyoyin hulɗar bretagne da Nijar, inda tarbiyya tatali take da matsayin cikakken mamba, sun shirya wasu ayyukan cuɗayyar al’adu a ranar 22 ga watan nobamba 2007, tare da tallafin “Bretagne’’ da birnin ‘’Carhaix’’
An nuna kaya na magoya bayan tsarin hulɗar Bretagne da Nijar, da hotunan sassan yanayin ƙasar Nijar, da ire-iren al’adunta, da waɗanda suka shafi fannoni daban daban kamar kiwon lafiya, da ire-iren cimaka, da ruwa, da sauran su, da hotunan ƙungiyoyi da ayyukan da suke gudanar.

A fannin jarida

An yi nazari bisa al’amurran da ke wakana a Nijar kamar tashe- tashen hankulla a arewacin ƙasar.
Akwai kuma ƙasidu iri-iri masu fahimtarwa bias yadda ƙasar take ciki.

A fannin harsunan gida da al’adu

An yi zaman tattaunawar tsakanin ƴan Nijar da ƴan Bretagne bisa halin amfani da harsuna daban daban a lokaci guda, kamar yin amfani da faransanci da harsunan gida a cikin makaranta, da cikin rayuwar yau da kullum, a faransa da Nijar.

Zaman taron yara

Yin ƙyallayen ado, gatannai

Kokowar gargajiya irin ta Bretagne ɗa irin ta Nijar

Sai a ɗauko ƴan kokowa huɗu na Nijar da makaɗinsu, da kuma ƴan kokowar ‘’Bretagne’’, ana nuna fusa’o’in kokowa. Ana nuna kayan ‘’Gouren’’ da na ƙungiyar yankin, da ‘’filim’’ na gajeren lokaci mai yin bayanai bisa kokowar gargajiya.

Nunin ɗunke- ɗunke

Samari da ƴan mata suna nuna irin ɗinke- ɗunken jahohin Nijar da na faransa.

Gatannai

Malama Fatsima Agali, mai gatana ta ƙasar Nijar, da wasu 2 masu gatana na ‘’Bretagne’’, sun gabatar da gatana da harshen faransanci da na gallo, da ƴan wasan kwaikwayo na ‘’lisen’’ Carhax da ke karanta gatannan hausa tare da maida su wasan kwaikwayo.

Abinci irin na ƴan Nijar

Ƴan Nijar da ƴan faransa sun haɗu , sun yi dahuwa irin ta afirika wandda mutane wajen ɗari biyu suka ci.

Kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe

Makaɗan zamani na ‘’Bretagne’’ da na Nijar sun yi wasa inda suka nuna al’adun kowace ƙasa ; akwai ‘’Makiɗa palabre’’, da ‘’Mamar kassey’’, da « Désert rebelle’’.

Makida Palabre