Wannan aikin ya bi matakai biyu na hadin gwiwa tsakanin Cesson-Ɗankatsari (na lokaci 2009-2013 duba nan, don aiki na lokaci 2013-2016 duba nan)
Manufofin Ci-gaba mai Dorewa
Ƙungiyar ta duniya ta ƙayyade abubuwa 17 na ci Gaban (SDG for Sustainable Development Goal), ciki har da :
- SDG 1: kawar da talauci a dukan siffofinsa da kuma a duniya
- SDG 2: kawar da yunwa, tabbatar da abinci, inganta abinci da inganta aikin noma
- SDG 3: Tabbatar da yaruwa a cikin zaman lafiya da kuma inganta zaman lafiya na dukan mutane gaba ɗaya
- SDG 4: Tabbatar da kowa ya samu daidaitattun horo da ilimi masu kyau da kuma inganta rayuwar ilmantarwa har kullum
- SDG 5: Karfafa daidaito tsakanin jinsi da kuma karfafa dukkan mata da ’yan mata
- SDG 6: Tabbatar da kowa zai samu yin amfani da ruwa, da tsabta kuma da tabbatar da tafiyar da samun waddanan abubuwa har kullum.
- SDG 7: Tabbatar da kowa zai samu amfanin makamashi na zamani da farashin mai araha wato cikin nasuwa
- SDG 15: Yi hamayya da kwararowar hamada, dakatar da sake juya tsarin lalata ƙasa
- SDG 16: Taimaka wa wajen ci gaban zaman lafiyar al’uma da kuma kafa cibiyoyi aiki masu mahimmanci a koina.
Ayyukan da ake son shiryawa a Ɗankatsari
Za su farawa cikin rani na shekara ta 2017 kuma sun hada da wadannan abubuwa :
- SDG6 kulawa da samun ruwa : horon masu tsabta da kuma masu bankunan kuɗi na CGPE (kwamitocin masu kulawa da samun ruwa), gyaran wurin samun ruwa goma da rijiyoyi bakwai, da kafa wani karamin wurin samun ruwa don kauyuka da dama na Nakigaza da kuma don yin sabin rijiyoyi uku.
- SDG6 game da tsabta : ginin salangogi don ƴan mata / maza a makarantun kwaleji bakwai
- SDG2, SDG15: Gyaran wurin sa kayan lambu na Marake Rogo, gandun lambun na ma’aikatar magajin gari, da kuma na makaranta.
- Aikin SDG7 lantarki: kafa wuri biyu na anfani da lantarki
- SDG5, SDG1,SDG3: horon ungozomai, horon mata don kulawa da tsarin iyali a kauyuka, horon yaki da jahilci, ba da bashi ga matan da aka hora, horo don kulawa da nauyin iyali.
- SDG4: horon malamai, samun kayan aiki da litattafai a cikin makarantu.
- SDG16, SDG2, SDG5 taimakawa ma’aikatun magajin garuruwa, bankunan hatsi, injin mika
Abokan aiki
An samu yarjejeniyar MAE, ta yankin Bretagne, ta jihar, ta kungiyar ruwa ta Bassin Rennais, ta Renes Métropole da kuma ta Loire Bretagne. Babban gudunmawar za ta fito ne daga jihar Nijar (45%) da kuma wajen mazaunan garin.
Cesson-Sévigné za ta taimaka wa wajen samar da kudade a shekara ta 2017 tare da ragowar yarjejeniyar haɗin gwiwa da Dankatsari na tsawon shekaru uku wato daga 2014-2017.
Hanyoyin sadarwa sun ba da damar yin fim mai sunan « ’yan mata uku a Dankatsari » na Idi Nuhu da Maman Siradji Bakabe.