A Nijar, mata suni fi fuskantar talauci da wasu matsaloli iri-iri na bambance-bambance tsakanin su da maza ; misali a fuskar dokoki.
Mene ne manufar yarjejeniyar ’CEDEF/CEDAW’ ?
Mahimmin kundi ne na dokokin Yarjejeniya game da duk wani halin
Nuna ma mata bambanci (CEDEF/CEDAW) suke fuskanta dangane da maza, wanda Majalisar d’inkin duniya ta amince da shi.
Ƙ asar Nijar ta amince da kundin, amma banda wasu matakai ; su ne a game da shekarun isa aure ga ƴan mata, da daidaici tsakanin mace da namiji a game da gado da ƴanci na mace ta zaɓi gidan zama, da ƴanci na mace ta ƙayyade adadinɗiya.
Maimakon yadda ayar doka ta 16 ta ambata, ita ƙasar Nijar ba ta amince ba da bai wa maza da mata ƴanci daidai, wajen ƙayyade yawan haifuwa da tsakaita haifuwar, da wajen zaɓen suna, da wajen rabuwar aure da cikin zaman auren.
A fahimci yarjejeniyar ‘CEDEF/CEDAW’
A albarkacin zagayowar sallar mata na duniya baki d’aya, ta ranar 8 ga wantan maris 2009, ƙungiyar Tarbiyya Tattali ta wallafa wani mahimmin littafi mai sunan ‘’A ’Fahimci yarjejeniyar ‘CEDEF domin ƴan Nijar, maza da mata, su ida fahimtar dukan ayoyin doka da yarjejeniyar ta ƙunsa, kuma ƙasar ta Nijar ta jaye ra’ayoyinta na rishin amincewa da yarjejeniyar. Saboda haka aka wallafa littafin tare da ba
Shi fuska 2 :
Za a yi gwajin yaɗa yarjejeniyar a cikin jahar Doso, tamkar littafin karatu na ƴan yaƙi-da-jahilci, inda za a fi bada ƙarfi ga karanta hakkokin mata. Yarjejeniyar ta ƙumshi ayoyin doka 30 da aka fassara cikin Hausa da Zabarmanci, tare da had’a su da hotuna wad’anda ba su saɓa ma al’adu ba.
Ana dogara da makarantun yaƙi-da-jahilci, da gidajen radiyon jahohi domin mutanen karkara su fahimci abin da yarjejeniyar ta ƙumsa, kuma a sumu hanyar ciyo kan ƙasar Nijar don ta jaye matsayinta na rishin amnincewa da wasu dokokin yarjejeniyar.
An wallafa fannonin 2 na yajejeniyar tare da taimakon Asusun da ke ƙoƙarin kawo daidaito tsakanin jinsinan 2, da taimakon ofushin Ministan Kyautata rayuwar mata da yara, da na sassan m’aikatun ofushim Ministan ilimi, da kuma asusun taimakon al’umma na majalisarɗinkin duniya.
Tunda akwai mafasarta yarjejeniyar a cikin sauran harsuman ƙasa, ƙungiyar Tarbiyya Tattali tana fatan samun tallafi daga abokanta na huld’a masu ganin an yad’a ta a duk fad’in ƙasa , birane da ƙauyuka.
A karanta jaridar ‘’sahel dimanche’’ ta ranar 6 ya watan maris 2009.