Ayyukanmu a makarantun boko, suna nuna kulawar ƴan makarantun ƙasar Faransa a game da matsalolin hulɗar ƙasashen Arewaci da na kudanci.
Mai yiyuwa wagga kulawa ta zama ginshiƙin girka cikakken fannin koyarwa da taimakon juna.

Saduwa

Mambobin ƙungiyar sun yi zaman tattaunawa cikin makarantun bokon da suka buƙaci haka, tare da halartar ƴan Nijar da ke zamne a garin Rennes, ko kuma masu wucewa. Awa biyu ake ɗauka domin mu gabatar da yadda ƙasar Nijar ta kasance a fannin kwancin muhallinta, da tarihinta, da tattalin arzikinta. Muna gabatar da ayyukan da ƙungiyar take gudanar da su a fannin makarantu, da kiwon lafiya, da al’adu. Muna nuna ‘’filim’’ na hotuna, muna bayar da bayyanai a rubuce, kuma muna canjin ra’ayoyi ta hanyar tambayoyi da amsoshin ƴan makaranta. Bayan haka, makarantar tana kawo abin ‘’bideyo’’ don a ɗafa na’ura mai ƙwaƙwalwa da muka kawo.

Tsare-tsaren karatu da fusa’o’in koyarwa

Wannan saduwar ta farko tana iya buɗe hanyar gano wasu abubuwa cikin « kwaleji’’ ko kuma a ayyukan mutum na kansa a cikin ‘’Lise’’. Abin da tsare-tsaren suka ƙumsa ya dace da tsare-tsaren ajin farko na ‘’Lise’’ a kan horon zama cikakken ɗan ƙasa, da na fannin shari’a, da zamantakewa.

Ayyukan cikin makarantu

Saduwar tana iya kaiwa ga gudanar da ayyukan ‘’kulob’’ masu bada damar canje-canje tsakanin Nijar da ƙungiyoyi masu taimakon makarantunta. Ayyukan ‘’Kulob’’ da ya kamata ƴan makaranta su ɗauki nauyinsu, suna iya dogara ga karatu ko wasan kwaikwayo bisa gatanan da ƴan makarantar ƙasar Nijar suka rubuta, ko bisa baza-kolin hotuna, ko sayar da kayan aikin hannu a lokacin mahawara bisa ƙasar Nijar.

Misalan ayyuka

 • Ita kuma lakkwol ɗin Bourgchevreuil ta Cesson a shekara 2011 ta saɗu da AESCD da aji 7 domin taimaka ma jariran Dan Katsari.
  An maimaita wannan aikin a shekarar 2013.
 • Lakole ɗin Beausoleil ta Cesson : 2012 shaduwa da AESCD tare da duk ƴan makarantar, yi da saida kayan marmari kamar su kyat da ƴan makaranta ke yi, don taimakon lambun makarantar Dankatsari.
  Wakilan ƴan makaranta sun ba Mahamadu Saidu wakilin Tarbiyya Tatali na Nijar cak na euro 452 lokacin da ya biyo Cesson a watan juni 2012.
  Ƴan makaranta suna yi da saida kyat don taimakon lambunsu na Dankatsari.
  An maimaita wannan aikin a shekarar 2013 da 2014.
 • A shekara ta 2016, Maman Chadau ya gana da wakilan dalibai na makarantu uku na Cesson da kuma babban gidan taimako « Relais Solidaire » saboda Dankatsari mai dalibai fiye da 800 na Cesson. Bayan da aka yi wasan gudu, kusan euro 3000 aka tattara. Wannan kudin zai sa a yi alluna da kuma bencina 60 cikin makarantu uku a yankunan karkarar Dankatsari. Aji na 5 na primary na Cesson sun fara musaya ra’ayi da wani ajin Dankatsari. An ci gaba da yin wannan aikin a shekarun 2017-2018 da 2018-2019.
 • Kwalejin Burgchevreuil na Cesson: Sekarar 2016 taron haduwar azuzuwan uku na masu shekara biyu a kwaleji bisa samun ruwa a Dankatsari gaban wani kwararen dalibi a fannin neman ruwa a kasa da kuma cikin duwatsuna na ANIRE. An kuma nunawa taron, fim na ruwa sun samu a Lugu. Sa’an nan karshen 2016 an sa hannun a kan wata yarjejeniya tsakanin kwalejin da AESCD da kuma sabuwar ganawa da azuzuwan uku na masu shekaru biyu a kwalejin lokacin ziyarar Mamane Chadaou a Cesson. An tsara musayar rubutu tare da kwalejoji uku na yankunan karkarar Dankatsari, haka ya sa aka samu (euro 350 ) don sayen kayan aiki kamar alluna da kuma bencina a makarantar firamare ta Lugu. A shekarun 2017-2018 da 2018-2019, ci gaba da tarurrukan tare da daliban aji biyu na kwaleji game da nuna musu fina-finai na Lugu ya samu ruwa falalla da na ’yan mata uku a Ɗankatsari.
 • Kolejin Orgeres a shekara ta 2019: taron koli na aji 6 masu shekaru biyu a koleji tare da nuna fina-finai kamar Lugu ya samu ruwa da kuma ’yan mata uku na Ɗankatsari, da tattaunawa.

Misalan ayyuka

 • Saduwa da malaman makarantar ‘’kwalejin’’ Betton : mahawara a kan ƙasar Nijar.
  Saduwa a ‘’Lise’’ na cesson, da ‘’Kwalejin’’ Betton, da Cancale, da makarantar Pace : mahawara a kan Nijar ta hanyar hotuna.
 • Saduwa a ‘’Lise’’ Loënnec tare da ƙungiyoyi daban daban dangane da zagayowar ranar yaƙi da talauci. Finafinai bisa Nijar, da saide-saiden katoci a ‘’Lisen’’ Bréquigny tare da ban hannun ‘’Aide et Action’’. Saduwa a makarantar ‘’Pace’’.
 • Hulɗa da makarantar sakandare Jean Jaurès ta Renne. A shekarar 2006-2008 sa hannu game da aikin samun keke 500 don kasar Nijar,gyare gyaren kekunan, Kiɗe kiɗen yan sakandare « taimakon Nijar » . Daga shekarar 2011, taimakon daƙin na’urar saƙon yanar gizo shirin tautaunawa tsakanin yan sakandaren Nijar da na Faransa, misali nufinsu game da Afirka, sarrafe sarrafen yan sakandare na matani, na wakoki, da video. A shekarar 2012 nuni « ci da ‘yan Adam, gurin ƙarni » aron CASDEN.
 • Koyarwa bisa fannin halayen zama cikakken ɗan ƙasa, da na fannin shari’a da zamantekewa a cikin azuzuwa huɗu na ‘’Lisen’’ Cesson. A shekara 2010 ƴan lycen Cesson, da ƙungiya saduwa ta Afrik Insa sun ba da raskona akan balagoron aikin da suka yi a Dankassari
 • A ‘’Kwalejin’’ Canale : tarbacen kuɗi dangance da tsarin ‘’une course pour le Niger’’ mai ɗaukar nauyin kafa ɗakunan littattafai a ‘’kwalejojin’’ Dogon Dutsi, da na sadarwa da ƴan makarantun ‘’kwaleji’’. ‘’Lisen’’ Brequigny : tarbacen kuɗi domin ayyukan ‘’hurojen’’ kiwon lafiya.
 • ‘’Lisen’’ saint Martin : ayyuka da yawa tun shekara ta 2005 ; kamar tarbacen kuɗin sayen shinkafa (‘’opération bol de riz’’), jaridar ‘’Lise’’, tarurrukan bada bayanai a lokacin makon haɗuwar ƙungiyoyi, tarurrukan ƙarin sani a shekara ta 2008 bisa littafi mai sunan ‘’Lugu da Sarauniya’’, kuma a shekara ta 2009 bisa karin maganganu na Nijar. A shekarar 2009, 2010 da 2011 kamacin bara kokon shinkafa dan hapkar da spiruline domin taimakon yaran Niger masu tamowa, yan makarantar Faransa sun ɗauki niyar shan kokon shinkafa guda rak domin tara kuɗin da za su taimako.
 • Ita kuma lakkwol ɗin Plélan le Petit et lycée Saint -Joseph de Fougères suka kwaikwayi haka da badar da spiruline ga yaran Niger da ke fama da tamowa.
Photo d’Alain Roux