‘’Asusun kawo canjin matsayi’’ : hulɗa ce tsakanin RAEDD da ƙungiyar Stromme

A Nijar, talauci yana cikin karkara kuma dawajen mata

A fahintar ƙungiyar RAEDD, matan karkara sun gogu, suna da ƙwarewa kan wasu ayyuka. Ta sha taimaka wa mata da yawa ga ayyukan tattalin arziki, kamar farfaɗowa da aikin saƙa, da na kaɗin zaren kaɗa a garin Lugu, da ƙara wa matan Wasa-da-hatsi hamzari wajen aikin raya wurare.
Ƙungiyar Stromme ta yi fatan yaɗa tsarinta na ‘’Asusun kawo canjin matsayi’’ a Nijar ; da farko a Burkina Faso da Mali ne take gudanar da shi.
Gurin wannan tsarin shi ne ƙarfafawa da inganta tsare-tsaren mata wajen kafa asusun kansu, da ƙa’idance halin bai wa kansu bashi, da sanya hannunsu cikin harakokin ƙungiyoyi da na mazamninsu. Ƙ ungiyar stromn ta nemi saƙa hulɗa da ƙungiyar RAEDD, wadda ta samu babban sakamako a game da makarantun da ake ce ma ‘’classes passerelles’’ a turance, wato inda ake ba yara wata sabuwar sa’ar ci gaba da karatu. Don haka ne ƙungiyar ta kafa tsarin ‘’Asusun kawo canjin matsayi’’ tun shekara ta 2009, a Ɗankatsari, da Dogon Dutsi, da Dogon ƙirya, da kiyeshe, da Matankari, da kuma Sukutan na Dapartaman Dogon Dutsi.

Dacewa ta farko

Gurorin da ake son cin ma masamman a shekarar farko, su ne :

  • Taimaka wa matan karkara don su yi ƴan ƙungiyoyin cuɗayyar juna ;
  • Ƙarfafa musu fusa’o’in tattali don su samu damar juya kuɗin asusunsu da kyau ;
  • Sanya musu hannu don su yi tsarin bai wa kansu bashi mai ruwa a cikin asusunsu, domin yin wasu ayyukan neman kuɗi ;
  • Horar da mambobin ƙungiyoyin cuɗayyar juna don kyautata lafiyarsu da halin rayuwarsu ;
  • Jawo hankalin abokan hulɗa na cikin yankin, kuma waɗanda suka yi na’am da tsarin, domin su bada hannu a ciki.

Sakamakon da ake neman samu a shekara ta 2010, shi ne :

  • Kafa ƴan ƙungiyoyi 120 ; kowacce ta ƙumshi mata 25 ;
  • Sanya mata 3 000 cikin gudanar da tsarin ;
  • Kafa asusun miliyan 14 da jikka 400 daga wajen matan da ke cikin tsarin (kowacce daga cikin matan 3000, ta riƙa zuba dala 100 kowane sati har sati 4 na wata 1, kuma cikin wata 12).
  • Ya zamanto matan ne aka ba bashin aƙalla na kashi 80 cikin 100 na kudin asusun ;
  • Aƙalla kashi 50 cikin 100 na matan da aka waye wa kai, suna yin amfani da gidan sabro ;
  • Kawacce daga matan 3000 tana iya bayyana hanyar kamuwa da masassarar cizon sabro, a gaban jama’a.

Za su sanin abubuwa da yawa bisa harakar ƙungijoyi ;

  • Za su koyi yin tsimi ko kafa asusun tsimi, da ka’ idojin bada bashi daɗaukar shi, da gudanar da ayyukan neman kuɗi ;
  • Za su yi sani bisa fannoni daban daban, balle bisa fannin kiwon lafiya, masamman ma bisa wata cutar da ta fi ƙanjamau ko ‘’sida’’ kashewa ; ita ce masassara cizon sabro ;
  • Za su yi lura da suna iya magana gaban jama’a ba tare da jinɗari ho damuwa ba, kuma suna iya shiga jerin mutane masu yanke magana a garin.

Da yake ƙungiyar RAEDD tana da gonar tsiron maganin tamowa a Dogon Dutsi, hurojen zai ƙumshi fannin bada bayyanai a kan tamowa da hanyoyin yaƙar ta.

Shekarar 2010 da 2011

A watan yuni ta shekarar 2010, an samu sakamako kamar haka :

  • Kafawar ƙungiyoyi 151 ;
  • Mata 3715 suka sa hannu cikin wannan shirin ;
  • Kafa asusun CFA na 18 000 000 F
  • A ciki, kashi 88 bisa 100 ake ara wa matan ƙungiyar.

Karshen 2011 wannan projet ya bazu a cikin ƙananan gundumomi 19 na gundumar Dogondutsi.

A shekara 2011 an samu raskona kamar haka:

  • Mace 7 154 na ƙungiyoyi 279 da suka fara aiki da samun horo da malaman EPC
  • Mace 5 877 membobin ƙungiyar, da suka samu bashi
  • Tsabar kuɗi da aka samo tatashi jimila 56.942.640 FCFA da timi 42.684.675 FCFA ;
  • Tsabar kuɗi mahinma da 49.099.480 FCFA na bashi kamar wajen kashi 86 cikin ɗari da matan suka tara da kuma aka biya.

A shekarar 2013 wannan projen na cikin ladunan dogonduci (Dogonduci, Dankassari, Dogonduci, Dogonkiriya, Kiéche, Matankari et Sucucutane) Tibiri (Tibiri, Dumega, Guéchémé et Koré Mairua.)

Projen EPC yakan gudana cikin garuruwa 145 bisa 471 da lardunonin biyun da suka kumsa. Akan haka ne shirin ya kafa gungu 494. An horatar da gungu 293 kuma wasu 201 suke cikin yin horo. Gungunan sun kumshi mata kimanin 12 307 cikin su akan samu mace 6 892 da suka dace da bashi. Addadin gungun ya fi samar da kudi kimanin 92 819 018 CFA bayan sayar da juyawa 70 566 285 CFA.

Kotamci

Madame Meri Gado ba ta je makaranta ba. Amma memba ce a cikin kungiyar Taimakon Kai da kai ko mu taimaki juna da ke garin Matankari. Tana da aure tun shekara hu’du da ‘diya mace biyu. Mijinta yana sana’ar saida kaji. Suna rayuwa ne bakin gari. Lokacin da ba ta yi aure ba mace ce shuru-shuru da gidan babanta ma ba a jin maganarta balle ma abukai. Wata rana tana hucewa sai ta hangi taron mata na kungiyar EPC. Da abun ya birge ta sai ta ce ita ma tana so ta shiga cikin wannan ƙungiyar. Bayan ta samu shiga cikin wannan ƙungiyar, ta kan rigayo kowa wajen taron mako-mako sannu sannu sai ta zam a mahimmacciyar mamba mai kwanzo. Domin haka ne aka samu walwala cikin rayuwar gidan nata. Kambacin wannan ne Meri take gurin ko wacce mace ta yankin nasu ta samu irin wannan don taimaka ma kansa.

Groupe d’épargne