Bayyana mana labarin fim dinki “Bisa sawun Mamani Abdulaye” wanda yake abin girmama wa marigayi mahaifinki ...
Ya fi a ce Nema ne. Ban san mahaifina sosai ba, an haife shi a Zinder a shekara 1932. Lokacin da ya rasu a shekara ta 1993, ina ɗan shekara goma kawai. Kasancewar ban san shi da kyau ba ya sa na yi fim ɗin nan. Ina so in bi sawun mahaifin nan da nake ƙauna.

Kin yi jiran dawowarsa…
Muna zaune a Zinder, mahaifina ya bar gida don zuwa babban birnin Yamai don karɓar kyautar rubuce-rubucen Bubu Hama da Nijar ta ba shi. Ya mutu akan hanya yayin da zai je amsar kyautar sa. Ya yi mana alkawarin ni da‘yan uwana mata cewa zai dawo mana da’ yar tsana. Na yi jira tsawon lokaci dawowarsa da ’yar tsanar da ya yi mana alkawarin ta, amma bai sake dawowa ba. Ina girma ina jin rashin mahaifin nan nawa.

Mamani Abdulaye sananne ne a matsayin marubuci…
An fi samin shi sosai game da rubutun wani labari da ya yi mai suna Sarauniya, wanda aka buga a 1980. Labarin wata sarauniya ce wacce ta kasance mai adawa da aikin Voulet-Chanoine, ta zama mai gwarzo game da yaki na mulkin mallaka. Wannan littafi na daga cikin tsarin karatun makaranta, kuma ana nazarin shi a jami’a. Ya kuma rubuta kirari, wakoki, wasan kwaikwayo, da sauran litattafai.

To menene aikin a siyasa?
Ta hanyar mutanen da na sadu da su, na sami labarin cewa shi ɗan ƙungiyar ƙwadago ne a shekarun 1950s, kuma memba ne a parti progressiste nigérien(PPN). A 1956, yana da shekara ashirin da biyar, an zabe shi, ya zama ɗan majalisa na jihar Zinder na partin Sawaba, wanda aka kera shi bayan rabuwa da PPN, sannan wakilin Jamhuriyar Nijar kan Babban Majalisar Faransa ta Yammacin Afirka a Dakar. A shekarar 1960, lokacin samun ’yancin kai, wadanda suke kan karagar mulki sun haramta Sawaba. Mahaifina ne daraktar jaridar partin da ya yi yaƙin samun mulkin kai ta hanyar cewa a’a ga Janar de Gaulle. Sadoda haka aka yi menan sa don a kashi shi, ya tafi gudun hijira a Algeria, a lokacin, Makka ta masu neman juyi. Ya yi aiki a rediyon Algerian har ya zama mai horo a makarantar aikin jarida a Alger. Ya dawo ƙasar Nijar a ƙarshen shekarun 1970, ya duƙufa kan aikin rubutu.

Mene ne kike tun rasuwar mahaifinki a shekarar 1993?
Na ci gaba da karatuna na yau da kullun. Lokacin da ya rasu ina makarantar primary a aji biyar. An haife ni a Zinder kuma a can na girma, sa’an nan na ƙaura zuwa Yamai.
Bayan Baccalaureate na yi karatun digiri a harkar kasuwanci. A 2008, na ga a cikin jaridar “Sahel” kira don aikace-aikace don foran mata goma da suke son yin finafinai. Na dade ina son yin fina-finai, amma ban san yadda zan yi ba. An zaɓe ni kuma na yi darussan rubuce-rubuce da yawa. Sannan na samu ra’ayin yin fim game da mahaifina, domin na riga na rubuta wani takaitaccen labarin game da shi.
Na yi rajista a Cibiyar Horar da Ilimi a cikin Ilimin Watsa Labaru da Sadarwar (IFTIC) kuma na sami lasisin a cikin samarwa da sauraron sauti. Fim na, Hawan Idi, ya lashe kyautar fim mafi kyau a Fespaco (Panafrican Film da Telebijin na Ouagadougou) a 2013. A 2014, ina zaune a Faransa a Annecy game da wata yarjajeniya da Fim ɗin Cinédoc kusan shekara guda don haɓaka shirina akan mahaifina.

Ta yaya kika gina labarin “Bisa sawunn Mamani Abdulaye”?
Na sha wahala wajen neman wuraren tattara bayanan. Na ɗauki shekaru goma wurin yin bincike, rubutu, harba da shiryawa. Na fara shi a cikin 2008 kuma na gama shi a cikin 2018. Aikin akwai wahala, amma niyyata mai yawa ce.

Ta yaya aka karɓi fim ɗin?
An karɓi fim ɗin sosai a Sifikiyar Cinema ta Afirka ta Duniya da Audiovisual a shekarar 2019, a Fespaco. Ranar 8 ga watan Yuni, 2019 ce ranar fitowar fim din a Yamai. Liyafar ta yi kyau sosai, ɗakin fim din ya cika kuma wasu daga cikin sahabban Mamani sun zo. Wannan dai shi ne karo na farko da ’yan Nijar suka sami labarin sa, saboda gwagwarmayar da ya yi a matsayin ɗan ƙungiyar cinikayya da siyasa ba ta cikin tarihin. Masana masu aikin tarihin Nijar sun taya ni murna suna cewa “kin yi aiki mai ban mamaki, yakamata a ce mun ne muka aikata wannan aikin, amma ke kika yi shi”.

“An yi nunin fim din « Bisa sawun Mamani Abdulaye”? a bukukuwan daban-daban, a Burkina faso, Suisse, Faransa, Algeria, Ghana, Rwanda ... An ba shi lambar yabo ta musamman a bikin kasa da kasa na silimar Alger. Wasu bukukuwa sun zaɓe shi, amma cutar Covid-19 ta sa an dakatar da nune nunen.

Ana samun “Bisa sawun Mamani Abdulaye” a kan replay bisa TV5.

Tattaunawa daga Nacima Chabani ta jaridar Elwatan da Marie-Françoise Roy ta Tarbiyya Tatali.

kafofin https://www.elwatan.com/edition/culture/amina-abdoulaye-mamani-documentariste-nigerienne-jai-longuement-attendu-le-retour-de-mon-pere-a-la-maison-23-11 -2019
Kundin tarihi: Bisa sawun Mamani Abdulaye

Hirar ta fito a Mujallar Tarbiyya-Tatali lamba 12 ([a nan → http: //forum.hopitalpsy.fr/tarbiya/IMG/pdf/magtt12.pdf])