Alichina Allakaye (a tsakiya bisa hoton da ke sama, wanda aka ɗauka a lokacin bikin Bagagi a 2021) shi ne ɗaya daga cikin wandanda suka kafa kamfanin wasan kwaikwayo na Les Tréteaux du Niger da kuma ƙungiyar fasahar Gamuart. Cikakken mai fasaha ne: mai zane, mai ban dariya, jarumi, darakta, ya samu horo da dama: daga 1982 zuwa 1985, horo na zane-zane a cibiyar al’adu mai sunna Umaru Ganda (CCOG) da ke Yamai a Nijar a karkashin inuwar kungiyar zaman lafiya peace corps. Ya koma wannan cibiyar a matsayin mai horar da zane-zane daga 1986 zuwa 1993. Daga 1994 zuwa 1997, ya yi horo a CCFN Jean Ruch da ke Yamai tare da fitattun ’yan wasan kwaikwayo, daraktoci da mawallafa na Faransa. A yau ya zama babban jigo a fagen al’adun Nijar, saboda sha’awar fasahar kere-kere da al’adu, amma kuma sama da haka, a shekarar 1982, a taron karawa juna sani na ustaz Rissa Ixa (mai zanen Nijer), a wajen taron karawa juna sani na Seydu Mumuni Maïga a Yamai, a cikin 1993. Alichina Allakaye ya baje kolin ayyukansa a Afirka, Turai da Amurka. Ya sa hannu cikin gidaje da dama na zane-zane: Tuluse (Saint Henri), Creil, Avignon (Faransa), Tahua, Zinder, Agadez, Yamai da kuma Yuri (Niger), tare da yin aiki a cikin wasanni da fina-finai da yawa.

Alichina ɗaya daga cikin wadanda suka shirya Faretin Bagagi ne a ƙarshen Agusta 2021 (duba Mujallarmu lamba 15).

Kuma ɗaya daga cikin mawallafin fim din “Akwai Magana! Za mu yi magana a kai."ne.