Abdulkarim Nassua wani matashi ne wanda ke zame a Yamai tare da cin amfanin zane-zanensa.

An fasara yadda yake tafiyar da ayyukansa a cikin shirin tahirin da aka zana zuwa ga tallakawa na Idi Nuhu .

A cikin aikinsa, yana amfani da dukan albarkatun al’adun gargajiya na Nijar domin ya nuna abubuwan da suka faru cikin rayuwar siyasa.

An yi nunin ayyukan Abdulkarim Nassua a RESIA a Saint- Brieuc a watan Nuwamba 2015 lokacin ziyarar Idi Nuhu .

Shugaban kasa Tanja a matsayin ɗan kokawar gargajiya

  • Halin da ake ciki : Shugaba Tanja ya take hakkin na kundin tsarin mulki don ci gaba da ajalin mulkinsa (Tazartche ) a shekarar 2009
  • Albadé Abuba , Ben Omar da Seini Omar : “Ga masu gado na gaske, lokacin Tazartche ! Baba Tanja, ƙare da su ka ci gaba da yin aikinka !”
  • Tanja Mamadu: “Na gaya maku ! Ba za ku iya yaƙi da ni ! Ina da goyon bayan ’yan ƙasa !”
  • Mahammadu Isufu • (shugaban kasar Nijar na yanzu) : “Ku taimake mu , don Allah ! Yana da karfi da yawa !”
  • Hama Amadu , “Ina ciwon ciki ! Baba Tanja, don Allah bar ni, in tashi !”
  • Mahamane Usmane , “Bari mu gudu kafin ya kai mana hare hare !”
  • Sanussi Tambari Jacku : “Ku ta shafa ! Ba zan yi jiran ganin karshen wannan abu ba !”