A yankin Illela, akwai wani hurojen da ke tafiyar da ayyukansa na ganin an cim ma daidaito tsakanin maza da mata a makarantun boko. Huroje ne na ‘’RAEDD’’ wanda yake samun tallafin kuɗi daga wata hukumar ƙasar Espana ta hulɗa da ƙasashe.
Dalilin kafa hurojen
Halin kawo bambance-bambance tsakanin maza da mata yana ƙara shimfiɗa talauci mai ɗorewa, kuma da done ma mata da ƴan mata hanyoyin shawo kansa. Idan kuwa ana son cin ma zamnannen ci-gaba, sai an kawar da ire-iren wad’anga matsalolin na ƙasƙanta mata, da rufe musu ƙofofin samun horo da wasu labarai, da hana su bunƙasa wasu ayyukansu, da ƙaurace su daga shawarwari da tsare-tsaren ci-gaba a cikin al’umma da iyalai.
Rishin muna bambanci tsakanin mata da maza yana cikin hanyoyin bunƙasa tattalin arziki da ci-gaban al’umma. A kan wannan ra’ayin ne ‘’RAEDD’’ ta kafa wannan hurojen da ke aiki dangane da yarjejeniyar murƙushe duk wata wariya da mata suke fuskanta (CEDEF/CEDAW). Ayar doka ta 16 ta yarjejeniyar, ta bayyana cewa mata suna da ƴanci daidai da maza a fannin aure.
Mata suna da ƴancin daidai da maza a game da duk abin da yake amfanin ɗiyansu (a misali, uba shi kaɗai ba ya da halin ɗaukar niyyar fitar da ɗiyarsu daga makaranta don ya aurar da ita; matarsa tana da ƴancin ƙiyawa)
Mata suna da ƴancin tsaida haifuwa ko tsakanta ta. Saboda haka, suna da ƴancin samun cikakkun bayanai bisa hanyoyin kare wanga ƴanci nasu (kenan suna da ƴancin shan ƙwayoyin magani ko yin alluran hana d’aukar ciki, ko kuma sanya hular riga-kafi).
Ta haka, wannan yarjejeniyar mai neman kawar da duk wata wariya da mata suke fuskanta, hanya ce ta shimfiɗa halin daidaito tsakanin maza da mata domin ba da damar zartar da ayyukan ci-gaba mai ɗorewa.
Sai dai, yaya za a iya cin ma wannan gurin idan aka dubi tsarin rayuwar al’umma da al’adu a ƙasar Nijar ?
Yawancin matasa na ‘’dapartaman’’ Illela waɗanda ba su ta’ba shiga makarantar boko ba, sukan tafi wurin diga a ƙasashen ƙetare. Daga sun dawo gida, sai aure-auren ƴan mata ƙanana, har ma da ƴan makaranta ; wasu ƴan digar ma aurensu na biyu ko na uku ne ; ko kuma su riƙa fasiƙanci da ƴan makarantar inda wannan hali yake sanyawa su bar karatun a dalilin ɗaukar ciki ko kamuwa da cutar ‘’Sida’’.
Aikin ƙungiyarmu shi ne waye kan ƴan maza da ƴan matan makarantun karkara don shirya cikakkun yara manyan gobe, da kuma waye kan uwaye don su tsaida aurar da da ƙanƙanan ƴan matan da ba su isa ba.
ƙungiyar ‘’RAEDD’’ ta san da akwai uwaye masu ɗiya mata a makaranta, amma suka fito da ciki.
Hakan ya sa ‘’RAEDD’’ ta samu fusa’ar tattaunawa da al’umma don uwaye su gane, su bar tabi’ar aurar da ƙanƙanan ƴan mata, kuma makarantu da sauran ma’aikatun da abin ya shafa kamar na yaki-da-jahilci, da na kiwon lafiya, da na sadarwa, su riƙa ba matasa cikakkun bayanai bisa duk abin da ya shafi haifuwa.
Ga ayyukan hurojen dalla-dalla
Gurinsa shi ne na ganin, a cikin ‘’dapartaman’’ Illela, ƴan mata ƙanƙana suna makarantar boko, kuma ba su fuskantar matsalar aure da ɗaukar cikin da ba a buƙace shi ba.
Domin haka ne hurejen yake gudanar da waɗannan ayyukan ; su ne : Taron waye kai bisa maganar shigar ƴan mata a makarantun boko. Taron waye kai da ƙarin ilimi bisa duk abin da ya shafi haifuwa, da tsare kai, da horar da al’umma.
Mahawarori tare da al’umma bisa matsalolin da ke fidda ƴan mata daga makarantun boko (ana yin mahawarar tare da mata daban, kuma tare da maza daban).
Wallafa abubuwan bada bayanai da na waye kai bisa mahimmancin bunƙasa horon ƴan mata.
Tsarin ayyukan waye kai kamar ta hanyar radiyon karkara, da ‘’bidewo’’, da wasannin kaikwayo, da mahawarori bisa fannin sanya ƴan mata a makarantun boko.
Kafa ‘’injinan’’ niƙa 3 saboda ƙungiyoyin mata
Taimaka wa makarantu da littattafai, da sauran kayan cikin makaranta.
An yi wani dan littafi don hukuncin iyali. Tun shekara 2009, da shi ne ake aiki don horo mallaman makaranta na firamare da na sakandare, a cikin aikin hulɗa tsakanin Cesson- Dan Kastari.
A shekarar 2014 an yi wa mallaman Matankari da na CFDC horo.
A shekarar 2015 an yi wa daraktan da mallaman makarantun Kieche Horo