An kammala wannan mataki.

Ɗakunan shan magani

Ga yadda tsarin yake a game da ɗakunan shan magani :
Gwamnati take gina ɗakin shan magani ; sai ta nemi al’umma da su tara jika 171 don sayen magungunna. Idan hakan ta samu, sai gwamnati ta kawo ma’aikatan da za su yin aiki a wannan ɗakin likitar, tare da kafa wani kwamitin tattali don karɓar kuɗin yin magani. Da kuɗin aikin da ake biya ne ake cike gurbin maganin da aka yi amfani da shi. Sai dai a wani lokacin, maganin yakan ƙarewa cikin wuraren maganin da yawa sai aikin ya tsaya. Dakunan shan maganin sukan rasa magungunna a lokacin alloba kamar ta zazzaɓin cizon sauro. Wani lokaci ma aikin kwamitin tattalin ba ya tafiya daidai.

Farkon ayyukanmu

Bisa kan abubuwan da suka faru ne, Tarbiyya Tatali ta ɗauki niyyar kafa tsarin ƙarfawa da ci gaba da gudanar da ayyukan dukan ɗakunan shan magani na ‘’dapartaman’’ Dogon Dutsi. An fara da garuruwa 5 masu ɗakunan shan magani ; su ne : Lugu, Bagaji, Anguwal Saulo, Kalgo, Kukabakwai. Tarbiyya Tatali (Aminnan Nijar) ce ta yi ɗakin shan magani na Anguwal Saulo, tare da taimako na wasu magungunna.
A shekara ta 2006, Tarbiyya Tatali ta ƙaddamar da wani bincike mai zurfi a cikin dukan ɗakunan shan magani 67 na ‘’dapartaman’’ Dogon Dutsi, mai ƙumshe da yawan mutane dubu 400.

Sakamakon binciken

Ɗakin shan magani 1, yana ɗaukar nauyin gari 2 zuwa 32 ; daga mutane 900 zuwa dubu 11 ; bambancin yana zowa daga gari zuwa gari. Kuma tafiya mafi tsawo da za a yi don cin ma ɗakin magani tana kaiwa kilometir 2 zuwa 25. Ana tara jika 165 zuwa miliyan 1 da jika 225 a cikin asusai : kenan a ‘kalla, kowane asusu ya yi tanadin jika 232. Kashi 30 cikin 100 na ɗakunan shan magani suna da tanadin kuɗi fiye da jika 200 ; kashi 33 cikin 100 suna da tanadin kuɗi tsakanin jika 100 zuwa jika 200 ; kashi 38 cikin 100 suna da ƙaramin tanadin kuɗin da bai kai jika 100 ba.

Bayan binciken, an kafa wani tsarin ayyuka na tsawon ‘yan shekaru domin ɗakunan shan magani na ‘’dapartaman’’ Dogon Dutsi ; su ne kafa kwamitocin tattali, bada taimakon magungunna, horar da malaman likita a fannin tsabta, da kuma horar da ungozumai.

Case de santé
{{}}