Tun daga shekarar 2020, ayyukan ANIRE sun tsaya cak. Don haka an cire ta na wani dan lokaci daga kungiyoyin Tarbiyya Tatali har sai an dawo da ayyukanta.

ANIRE, ƙungiya ce da ta ga rana ran 12 ga watan october 2013, ta samhttp://www.tarbiyya-tatali.org/ecrire/?exec=rubrique_edit&id_rubrique=175#u damar yin aikinta a jaridar J.O ta 15 ga watan maris 2014. Can da AENIRE (Ƙungiyar daliban Nijar na Rennes), ake kiran ta, yanzu ta zama ANIRE (Kungiyar ‘Yan Nijar na Rennes) bayan wani taro da aka gudanar a ranar 20 ga watan mayu 2017.

Gurinta dai ta tara duk ƴan Nijar da ke a Rennes. Kuma tana kira ga duka ƴan Nijar maza da mata. Maƙasudinta shi ne ƙirkira hili na taimako tsakanin membobinta, don tattaunawa, da sanin Nijar gaba ɗaya, da sa hannu don samun ƙyaukyawar rayuwar ƙungiyar Rennes, da ɓunkasa huldar Yamma/ Gusum.

Ayyukanta dai ana yin su ne cikin farin cikin da kwanciyar hankali, tare da tattalin taimakon juna waɗanda su ne arziki Nijar. Abubuwa na farko na wannan ƙungiyar su ne : haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan Nijar na Rennes da ƙarfafa haɗin kansu, tsare tsaren taro don tattaunawa da hira.

Tarbiyya Tatali tana ba da muhimmanci ga haɗin gwiwa tsakanin ’yan Nijar da ‘yan Faransa, a Faransa da Nijar. Musamman AECIN koyaushe mataimakin shugabanta na ƙasar Nijar ne, kuma akwai ‘yan Nijar masu kokari sosai cikin ƙungiyar. Tana da membobin ‘yan Jamhuriyyar Nijar da yawa cikin Hukumar Daraktocin ta. Yawancinsu ɗalibai ne, membobin ANIRE.

AECIN da ANIRE membobin Majalisar ‘yan Nijar ne a Faransa.

 

Articles liés

Archives