| français | English | Español |
Cikin harshen hausa, Tabiyya Tatali na nufin ‘’Taimako kan ci-gaban kai da kai’’.
Babban ma’kasudin wannan rukinin ’kungiyoyi a fannin makarantu na Nijar da na Faransa shi ne taimaka wa ’ko’karin da al’ummar Nijar ta ’dauki nauyin tafiyar da ci-gabanta mai ’karko, tare da yin kira ga taimakon ’yan ’kasa kuma da taimako daga ’kasashen duniya da kuma ba da kuzari ga sanar wa juna al’adun gargajiya.
Tarbiyya Talali ta ’kunshi : A Nijar, ’kungiyar RAEDD (Rukunin ’kungiyoyi ne mai kula da ci-gaba mai ’karko wajen ayyukan makarantu) ; A Faransa, ’kungiyar AECIN (’kungiya ce mai sanar wa juna al’adun gargajiyar tsakanin Ille da Vilaine Niger), ’kungiyar Aminan Nijar (‘’les Amis du Niger’’) da ’kungiyar AESCD (’kungiya ce ta taimakon juna tsakanin garin Cesson (a ’kasar Faransa) da garin ’Dankassari (a ’kasar Nijar)). A ’kasashen Faransa da Nijar, duka wa’dannan ’kungiyoyin suna neman abokan hul’da kuma suna tattara ku’din taimako. Suna sa hannu ga rayuwar ’kungiyoyi a ’kasashen Faransa da Nijar.
| A Nijar | A Faransa | |
| ’Kungiyar RAEDD | ’Kungiyoyi na rukunin ’kungiyoyin Tarbiyya Tatali. | |
| Tana nazari bisa halin da karkara take ciki. | Suna sa a san ’kasar Nijar, | |
| Tana yin huroje dabam-dabam, | Suna shirya taruwa da kula da abubuwan da suke faruwa, | |
| Tana yin ayyuka wuri ’daya. | Suna bi sau da ’kafa ayyukan da ake yi a Nijar. |
Abuta taskanin faransawa da ’yan Nijar.
Amana da girmama juna.
Sanin juna daga al’adunmu na gargajiya.
Rabo daidai taskanin juna.
Kiyon lafiya na mata da yara ’kanana
Taimako ya ’yan ’kasa masu ’kir’kiro ayyukan tatalin arziki
Tarihi da al’adun gargajiya na yankin Arewa
Ziyarce-ziyarce a kai a kai da aminai Faransawa suke yi a Nijar don su lura da ayyukan da ake yi.
Ziyarce-ziyarce da ’kungiyar RAEDD take kai wa a Faransa don ta sa a san ’kasar Nijar kuma ta sadu da mutanen da ake hul’da da su.
Organisation Tarbiyya Tatali
Accueil du site - Plan du site - contact - actualite
conception : Elise Coste - redaction : Marie-Francoise Roy, Mahamadou Saidou
RSS 2.0
| Espace privé
|