A cikin wannan yankin, Tarbiyya Tatali tana gudanar da ayyuka da yawa yanki ne da yake kuduncin ƙasar Nijar, a jahar Doso cikin gurbin wani tsohon gulbin da ya ƙahe da ake ce ma Dalol Mauri, kusancin iyaka da Nijeriya. Yawan al’ummar yankin dubu 400 ne, kuma ya ƙunshi kwamin 10 (Danƙatsari, Dogon Dutsi, Dogon ƙirya, Dumega, Gesheme, Kiyeshe, Matankari, Kore Mairuwa, Sukukutan, da Tsibiri). Dangance da tsarin rage cinkoson mulki, an yi zaɓen farko na kwansayye da magajojin gari ‘’Mar’’ a shekara ta 2004.

Dogon Dutsi

Dogon Dutsi ce babbar barikin yankin Arewa. Babban gari ne mai mazauna dubu 30. Sunan Dogon Dutsi ya fito daga wani babban Dutsi mai siffar babban shuri wanda ya kere komi, kuma ya yi ma garin dala.

Mutanen yankin manoma ne

Yawanci al’ummar yankin Dogon Dutsi manoma ne ; amma akan samun buzaye da hillani makiyaya. Da kalme ake yin noman hatsi, da dawa da wake, da kuma gujiya.

Wani halin rayuwa mai ban tsoro

Yaɗuwar al’umma da yawaita nome-nome ya jayo rishin nagartar ƙasar noma, kuma ga ƙarancin ruwan sama. Bayan haka, Hamada tana bunƙasa a dalilin tsananin amfani da icen tuya. Wani bajamushe mai suna ‘’Barth’’ a shekaru 140 da suka gabata, ya bayyana cewa yankin Arewa, gandun daji ne inda akan samun ‘yan wuraren noma. Yanzu haka wasu, kakannun suna tune da wannan sunƙurun dajin da namun daji da yake cikin sa. Amma a halin yanzu, Arewa ta zama busashen daji, sai hakukuwa da manyan itatuwa jehi-jehi, har ma dole sai matasa sun tafi cin rani ko tafiyar dindindin a birni ko ƙasashen kudu wajen biɗa.

Ingantaccen tsarin ƙungiyoyi

Ƙungiyoyi da yawa suke yin ayyuka a cikin yankin, kamar kwashe sharar garin Dogon Dutsi da tsabtace shi, da hurojojin dashen itatuwa, da tare ruwan ƙasa a cikin daji, da kuma ayyukan da tarbiyya tatali take gudanar.

Mahimmin tarihi da cikakkun al’adum gargajiya

Kokowa da ƴan mulkin mallaka da daidaicin ƴanci tsakanin maza da mata, su ne mahimman abuduwan tarihi da na al’adun Arewa. Garin Lugu ne cibiyar tarihin Arewa ; nan ne mazaunin Sarauniya.

Dogondoutchi la grande pierre