An fiddo wannan gatanar daga littafinmu na gatanai wanda ya ƙare mai sunan “A l’école des contes nigériens” wato “gatanan Nijar a makarantu”, kuna iya samun littafin na biyu mai suna ‘’Il était une fois au Niger’’ a cikin kantinmu.

Wata tsanantattar yunwa

Wata shekara aka yi wata tsanantattar yunwa cikin wani gari. Mato da ƴaƴansa da yawa suka rasa abincin da za su ci, sai ya tafi wurin Doguwa don samun rancen abinci. Doguwa ta ba shi rancen wani babban sa, har zuwa baɗi, kuma ta ce mashi :

  • Dan na zo, ina son ka ambaci sunana kawai a kambacin san da na ranta maka. Sunana na zane shi ne Cilo Cilo Mata Nakambari.

Sai Mato ya yarda kuma ya je ya sayar da san, ya sayo abinci.
Kullum Mato yana sanya ƴaƴansa suna maimata sunan Doguwar sau da yawa don maganin mantuwa.

A kwana a tashi, a ranar zuwan Doguwar, sai duk iyalin Mato suka mance wannan sunan na Doguwa. To, sai suka yi shawarar barin garin don tsoron hushin Doguwa ; suka ɗauki kayansu suka tafi. Da suka iso ƙarƙashin wani iccen tsamiya, sai matar Mato ta ce a tsaya kaɗan don ta ba jaririnta abinci. Sai suka ji jaririn yana cewa :

  • Cilo Cilo Mata Nakambari.

Dukansu suka yi mamaki, sai suka koma garinsu don su yi jiran Doguwa. Daga zowarta, ta ce :

  • Salama Allekum.

Mato ya amsa :

  • Wa Allekum salam
  • Mine ne sunana na zane ?
  • Sunanki Cilo Cilo Mata Nakambari .

Ko da Doguwa ta ji sunan, sai ta koma.

A nan ana son nuna cewa, kar a rena komi a duniyar yau, har ma yara ƙanana.

Gatana ce ta Nijar da makarantar Argum (cibiyar ƙananan makarantu ta Dagon Dutsi, IECB1) ta gabatar ga wasan gasar da ‘’Aide et Action’’ da kuma RAEDD suka shirya a bikin nunin al’adun gargajiya na gatan gatan.

Mai gatana : Malama kalle Dije
Ƴan makaranta : Ramatu Umaru, Rilwana Kalle, Bshiru Munkaila, Barak Issa, Sakina Maman. Malamai masu kula da tsarin : M. Usman Tamo, Malama Aliyo Salamatu

A l’école des contes nigériens