An kammala wannan mataki.

A shekara ta 2001, Tarbiyya Tatali (aminnan ƙasar Nijar tare da gowon bayan RAEDD), sun ɗauki nauyin wannan tsarin na tabbatar ma Kowane d’an makaranta na da littafi na kowane fanni a garin Goru Kirai.

Haɗa kiwo da karatun boko

Mazauna garin, hillani ne kuma kiwo ne aikinsu na yau da kullum. Uwaye suna shakkun sanya yaransu makarantar boko saboda suna tsoron sakin al’adu daga wajen yaran. Kenan dole sai an nemi hanyar haɗa kiwo da karatun boko.
A shekara ta 2002, aminnan Nijar sun ba ƙungiyar uwayen ƴan makaranta jikka 223 don kafa tsarin haɗa kiwo da karatu. ƴan makaranta 23 ne aka zaɓo a wala-wala a cikin ƴan aji na 5 da na 6, waɗanda aka raba ma jikka 10 kowanne. Da waɗanga kuɗin za su sayi wata dabbar da za kiwatawa cikin tsawon wata 5, kuma su sayar da ita don su biya bashin, tare da ɗora ribar kashi 10 bisa 100 na kuɗin bashin. Da ƙarin wannan ribar ne masu samun bashin suka kai 26 a shekara mai zuwa, kuma su kai ƴan makaranta 31 da jimillar bashin jikka 350. Asusun ƙasar kanada mai tallafa wa irin wannan ƙoƙarin, ya ida cike kuɗin, ta yadda dukan ƴan makarantar za su iya samun wannan bashin: a halin yanzu an raba miliyan 1 da rabi ga yara 201 (ƴan mata 103, da ƴan maza 98).

Kwamitin makiyaya

Ƙungiyar uwayen ƴan makaranta ta kafa wani kwamitin makiyaya wanda za ya kula da tattalin kuɗin ‘’tsarin haɗa kiwo da karatu’’. Kwamitin ya ƙumshi shugaba 1 ‘’Parzidan”, da mai ajiya 1, da magatakarda 1; dukansu uwayen ƴan makaranta ne da aka zaɓa har tsawon shekara 2. Banda wanga buron, akwai wani malamin RAEDD, kuma malamin makarantar ne, wanda yake da nauyin bin ayyukan sau-da-ƙafa, kuma ya rubuta wa uwayen ƴan makarantar takardun kira, da wa’adin bashin. Sai ƴan makarantar su biya idan lokacin ya yi, a wajen mai ajiya.
Ana ba kowane ɗan makaranta bashin jikka 10 da ake ganin za su isa sayen wata dabba da sayen dussar ciyar da ita. Shi za ya kula da bisarshi, da abincinta, da yi mata magani har tsawon wata 5 inda ya kamata iyayen su sayar da ita a kasuwar da take bisa hanyar garin Sayi, ko ga mahaucin garin. Wasu yaran sukan raka iyayensu don su ga yadda ake yin cinikayyar. A ƙarshen waɗannan watannin 5 ne kwamitin makiyayan yake kiran taron dukan uwayen, inda kowa za ya biyan bashinsa tare da ɗora ribar kashi 10 cikin 100 na bashin. Ya kamata a ce kuɗin sayar da dabbar sun zarce kuɗin sayo ta, har ma sun lumka biyu, wani lokaci
Ribar da aka samu ga sayar da dabbar, ta yaron ce shi kaɗai don ya sayi tufafi, da kayan aikin makaranta, da abinci a makarantar.

Yaya za a rage asarar?

Dabbar tana iya zowa da tsada (har jikka 10); komi ya danganta da lokacin da aka ɗauki bashin. Idan a lokacin da abincin dabbobi ya yi ƙaranci ne, to ana samun dabbar da rangwane sosai-yana yiyuwa kuma dabbar ta yi rishin lafiya ; ana iya saida ta, amma da araha ƙwarai (misali jikka 7), ko kuma ta mutu. Duk da haka, dole ne a biya bashin; amma ana iya ƙara wa’adin biyan in uwayen sun shaida wa kwamitin tattalin. Sau ɗaya waniɗan makaranta ya biya bashin dabbarshi da ta mutu ba tare da ya shaida wa mai bi sau-da-ƙafa ba. Kwamitin tattalin yana cikin neman hanyar sulhunta wa ƴan makarantar da asarar ta hau.

Conteuse et livre de contes