An kammala wannan mataki.

Haɗin kan ƙungiyoyi, ‘’REPTA’’

Haɗin kan ƙungiyoyi ne masu neman tabbatar ma kowa hanyar samun horo cikin Afirika. ‘’REPTA’’ ta ƙumshi ƙananan hukumomi na ƙasar Faransa da na Afirika, da wasu ƙungiyoyi (a cikin su akwai Tarbiyya Tatali), da kuma wasu masana’antu. REPTA tana gudamar da ayyuka a ƙasar Burkina Faso da ƙasar Nijar. A garin Bobo Diyulaso na ƙasar Burkina Faso, tana yin ayyukan horarwa da tarbiyantar da yaran da ke yawon banza, wato ƴan horon titi. A ƙasar Nijar, tana bada ƙarfi wajen samar ma kowane yaro halin shiga makaranta, da samun horo.

Ga ayyukan a ƙasar Nijar

Tun watan janairu na 2006, aka kafa aji 7 na makarantun sa’a ta 2 a garin Moli, da Akubunu, da Bumba, da Tondeyi, da kare kopto, da walam, da Diyaguru cikin jahar Tilaberi da ta Tawa. Aji ɗaya yana kar’bar yara ‘yan shekara 9 zuwa 13 waɗanda suka bar makarantar boko, ko kuma ba su ta’ba shiga ba ; shekaru 4 ne tsawon karatun, tare da gurin horar da su a cikin harshensu,da koya masu wasu ƙananan ayyukan hannu, da ci-gaba da karatu a ‘’kwaleji’’ ga wasu.

Abokan hulɗa na ƙasar Faransa da na ƙasar Nijar

Dukan azuzuwan 7 da makarantun jarrabawa ta 2, wasu jahohin ƙasar Faransa ne suka zuba kuɗin gina su. Su ne : jahar ‘’ Bretagne’’ (aji 2) ; jahar pays de Loire (aji 3), ta ‘’Basse normandie (aji 2). A Nijar kuwa, ‘’REPTA NIGER’’ da Tarbiyya Tatali (RAEDD) ne suke kula da aikin bi sau-da-ƙafa.

Hulɗa tsakanin RAEDD da aecin da kuma REPTA ta dakantarda aikinta tun allip dubu biyu da goma a kan ajin sa’a ta biyu ta garin Moli.

Boumba
Boumba