A farkon shekara ta 2018, ana ba da karamin bashi ga mata masu yaki da jahilci cikin tsarin shirye-shiryen “Ci gaba zuwa Burin Mai Dorewa a ƙauyukan Dankatsari” da kuma “Ayyukan haɗin kai don ci gaban karkara na ƙauyuka na Dankatsari 2021 -2023”. Wannan aikin na samun ƙaramin bashi yana samun tallafawar garin Cesson-Sevigne.

Na Guizara da Karkim Mallam

An kafa wannan tsari ne game da tambayar mata masu yaki da jahilci na Guizara da Karkim Mallam.

A farkon 2018,ana gudanar da ba da ƙananan basussuka a cikin tsarin shirin “Ci gaban manufofin garuruwan Dankatsari”. Rukunin hudu na mata 25 na garuruwan Guizara, Karmi Mallam, Kamrey da Dogontapki suka amfana da tsarin. Bashi na CFA jika 50 (kimanin euro 80) suke iya samu bayan sun biya jika 5, kudin shiga kungiyar kuma dole ne su biya kudin da aka ba su bashi cikin watanni 6.

Ana iya karanta labarin tauttanawa da tambayoyi na mata hudu da suka yi amfani da wannan tsarin a cikin mujalla ta 8.

An tsamo shi daga labarin Matsarar littafin Yaki da jahilci da ƙananan basussuka, Mujallar ta 8.

Wane irin aiki ne kuke yi mai kawo muku kudi ?

Mariamun: “Ina kananan sana’o’i, Ina yin tsalla ta hatsi da nike saydawa a makaranta ko cikin gari, ko a tasha, a duk inda ke da mutane. Don dai ba ni da hali sosai ne, da babban ciniki zan yi“. Sagni:”kiwon kananan dabbobin saboda rashin kudi sosai.“Fati:”Kamar sauran mata, kananan sana’o’i da kiwon kananan dabbobi ya fi a zauna ba yin kome.“‘yan cinjin kudi a karkashin matashin zai warware wasu matsaloli ko ba haka ba ne?” Zalfa: “Lokacin da aka ba mu bashin FCFA jika 50, (euros 80), mijina ya ce mani:”Ba a ba ki wannan kudi ba don zuwa bikin aure ko na suna ba; An ba ki su ne don ki yi ‘yar sana’a ko ki samu riba. Saboda haka dole ku yi hankali sosai. Kar ki sa mu kunya (idan ba ki biya ba). Don haka, game da shawarar mijina, ina kananan kasuwanci da sauran kuɗin bayan sayen karamar daba don kiwo. "

A Dogontapki da Kamrey

Fib 2018, Ana ba da ƙananan rance a cikin tsarin aikin “Ci-gaba mai ɗorewa a Dankatsari 2018-2020”. Ƙungiyoyi biyu na mata 25, masu karatun yaki da jahilci na ƙauyuka Kamrey da Dogontapki suke amfani da shi. Bashi na jikka 50 000 (kimanin euro 80) suke iya samu bayan sun biya kudin shiga jikka 5,000, kuma dole ne a biya su cikin watanni 6.

Tun 2019, ƙarfafawa da saka idanu

A karshen watan Agusta 2019, an kara darajar kudin bashi na jikka ashirin da biyar ga matan Guizara da Karki-Malan (jimlar mata 62). An tsara ba da bashin kuɗi na jikka hamsin ga kowace mace a Chanono don sababbin ƙungiyoyi biyu (mata 50). Chanono yanki ne na kiwo, kuma hillahirin mata suna yin irin wannan aiki (kiwon) na ƙananan dabbobi (awaki, tumaki) to, lokacin da aikin su ya bunkasa kuma, su yi kiwo shanu.

An yi aikin sa ido a kauyukan Kamrey da Dogontapki. Mafi yawan mata suna ƙauyukan gona saboda yawancin suna yin kiwo kuma suna yawo da dabbobinsu inda ciyawa ke da yawa.

A shekarar 2020, an kafa samun karamin bashi na jikka 50,000 CFA a Tunzurawa da Gofawa kuma tallafin ya karu zuwa jikka 75,000 CFA don tsofaffin kungiyoyin Kamrey da Dogontapki.

A cikin 2021, an kafa samun ƙaramin bashi na 50,000 CFA a Tudu Makera kuma tallafin ya karu zuwa 75,000 CFA ga tsofaffin ƙungiyoyin Chanono tare da ƙungiyoyi 2 da Tuzunruwa da Gofawa tare da rukuni ɗaya. 

Micro-crédit féminin à Dankassari