Kafa injin niƙan hatsi a Ɗankatsari

A Nijar, dakan hatsi aikin yau da gobe ne na mata su kaɗai, kuma yana gajiyar da su sosai.

Yawan ayyukan gida da ƴan mata suke yi, yana ɗaya daga cikin dalillan rishin yawansu a makarantun boko.

Girka injin niƙan hatsi, zai bunƙasa amfanin da ƴan ƙungiyoyin suke samu, kuma zai sulhunta rayuwar yau da gobe ta matan unguwa.

Wani bashi a cikin tallafin da kwamin ta ‘’Cesson-Sévigné’’ ta kawo, ya ba wata ƙungiyar mata damar sayen injin niƙan hatsi wanda aka girka a garin Ɗankatsari a farkon shekara ta 2009.

Idan aka biya bashin, sai kuma wata ƙungiyar ta yi amfani da kuɗin don sayen wani injin niƙan.

A shekara ta 2010, tahunonin niƙan hatsi 2 aka girka a garin Bawada Gida da kuma Lugu.

Shekara 2011 hulda ta taimaka ma Dogontapki da kamrey domin tallaha musu da injinan nikan hatsi.
A shekarar 2012, an kafa wata na’ura ta niƙan gero a Jarkasa.
A shekarar 2013, an kafa wata na’ura ta niƙa a Karkim Mallam, ta Lugu kuma an gyara ta, an ja hankalin mutane wajen kulawa da su.

A shekara ta 2016, bayan an yi nazarin wuraren bankunan hatsi na jihar an yi wani tsari na horo na dukan kwamitocin masu kulawa da injinan hatsi, haka kuma an yi tsarin horon masu kula da injinonin nan har da kayan aikin su. An yi gyaren injinan Dogontapki, Kamrey da Lugu an kuma kafa sabin injinan biyu a Burtu da Chanono.

Jeune pileuse