| français | English | Español |
Yau da kimanin shekaru 10 ne ’yan kokowar Nijar da na Bretagne suka yi saduwar farko a lokacin kasuwar baza-koli ta Saint Brienc da aka shirya albarkacin hul’dar da ke tsakanin Côtes d’Amor da Nijar, inda ’yan kokowar suka halarta. A nan ne aka samu cu’dayya tsakanin ’yan kokowar Bretagne da na Nijar ; sai dai cu’dayyar ba ta ‘dore ba daga nan.
An farfa’do da wannan hul’dar a lokacin wasannin na 2005, tunda akwai kokowa a cikin tsarin wasannin, inda ’kungiyar kokowar Faransa ta aiko ’yan kokowar Bretagne don ta wakilce ta. An yi nune-nunen fusa’o’in kokowa daga kowane ’bangare, hakan kuma ya ‘kara dan’kon amintaka tsakanin su. Hukumar ’kungiyar ’kasashen, da ’yan kokowar Faransa sun nuna gamsuwarsu da irin salon kokowar Nijar, kuma ’kasar ta Nijar ta yi farin cikin haka ; har aka fitar da wani littafi na mahimman hotunan wasannin.
’Da’din da mutanen Bretagne suka ji a wannan ha’duwar, shi ya sa ’kungiyar ’yan kokowar ‘’Gouren’’ ta yi ‘ko’karin gayyatar ‘yan kokowar Nijar don su halarci wani zaman horon ’yan kokowa na ’kasa da ’kasa a ‘’Carhaix,’’ cikin shekara ta 2007, kuma da wata kwam’balar kokowar gargajiyar ’kasar ‘’Ekos’’, tsakanin ’kasashe.

Publié le : dimanche 11 juillet 2010
Organisation Tarbiyya Tatali
Accueil du site - Plan du site - contact - actualite
conception : Elise Coste - redaction : Marie-Francoise Roy, Mahamadou Saidou
RSS 2.0
| Espace privé
|