An kafa aji 19 a cikin ‘ɗapartaman’’ Dogon Dutsi.

A shekara ta 2007, an buɗe aji 19 na yaran da suka wuce shekarun shiga makaranta; su ne: aji 9 a cikin kwamin ta Dogon Dutsi, aji 5 a kwamin ta Ɗanƙatsari, aji 5 a kwamin ta kiyeshe, da kuma aji 1 a Yamai.

A game da hulɗar tsakanin ƙungiyar ‘’Stromme’’ da ta Tarbiyya Tatali

An kafa wannan hurojen domin gudanar da ayyukan tsawon shekara 4 cikin hulɗa da ƙungiyar ‘’Stromme’’’ wadda aka girka a shekarar 1976 domin ta ci gaba da irin aikin da wani almasihu mai suna Olaf Kristian Stromme na ƙasar ‘’Norbejiya’’. Tun shekara ta 1960 ne shi stromm ya ba da kansa ga ayyukan ceton al’ummomin ƙasashen kudu masu fama da talauci. Ya girka wani sabon tsarin tarbacen kuɗin da suke kawo tallafi ga ƙungiyoyi da huroje da yawa masu ayyukan ci-gaban al’ummomi. ƙungiyar ‘’Stromme’’, ƙungiya ce mai zaman kanta, mai faɗi-ka-tashin shafe hawayen ɗan Adam. Tana kawo tallafi ga tsare-tsare da yawa a fannin noma, da kiwon lafiya, da samar da tsarkakkun ruwa, da tsabta, da horo, da kuma fannin al’adu da bunƙasa ayyukan hannu. Ba ita take aiwatar da ayyukan ba; sai dai ta taimaka wa ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasashe masu tasowa, a cikin ayyukansu na ci-gaba; kuma sai cikin ayyukan da aka tsara tare da al’ummomi kaɗai ne take saka kuɗinta.

Kowace shekara, ƴan makaranta 600 ake maidawa hanyar makaranta.

Hurojen yana bada damar maido yara 600 ƴan shekaru 9 zuwa 13 a kowace shekara ; ƴan makaranta 30 cikin kowane aji kamar yadda ƙungiyar ‘’Stromme’’ ya ƙayyade. Bayan shekara 1 cikin wannan ajin na masamman inda ake kashe jika 40 kan kowane yaro, sai ƴan makarantar su ci gaba a cikin makarantun gwamnati.

Koyarwa cikin harshen hausa da na faransanci

A cikin tsarin koyarwar, da harshen hausa ne ake tafiyar da ayyukan karatu da rubutu na tsawon wata 2, san nan kaɗan kaɗan a riƙa sanyo harshen faransanci. An san da cewa harshen hausa, harshe ne wanda ya yaɗu sosai a cikin Afirika ta yamma, renon Ingila ko Faransa, kuma shi ne harshen mafi yawan al’ummar Dogon Dutsi.

Sakamakon da aka samu a shekarar 2007- zuwa 2008

A ƙarshen shekarar farko, an samu babban sakamako. Dukan azuzuwan karatun guda 20, an kafa su ; kuma a cikin ƴan makarantar 600 da aka ɗauka, 574 sun riƙa zuwa makarantar sosai. Kashi 50 bisa 100, ƴan mata ne, kuma a cikin 48 bisa 100 suna zuwa kai-da-kai.
A wata jinjina da hukumar ƙananan makarantun gwamnati, da cibiyar kula da wad’annan makarantun na nassamman suka yi, ƴan makaranta 559 ne suka samu ci gaba da karatu; yawanci sun shiya aji na 4, wasu a aji na 5, wasu aji na 3; mafi yawa suka kuma suka rungumi koyon wata sana’a.
A cikin ƴan makaranta 24 da suka samu shiga aji na 5 a shekara ta 2008, 23 suka ci nasarar samun takardar ƙarshen karatun aji na 6 a watan juni na 2010.

An cim ma wannan babban sakamakon saboda jan ƙoƙarin dukan malaman da ke kula da makarantun, da su ƴan makarantar, da al’umma, da kuma magabata. Uwayen yara da ke cikin kwamitocin tattali, su ma sun taka mahimmiyar rawa wajen aikin waye kai.

Akin 2008-2011

Wurare 30 ke akwai na waɗannan makarantun a cikin kwamin ta Dogon Dutsi, da ta Ɗankatsari, da ta Iiyeshe. ana sake gari idan inda suke, babu sauran wasu yaran da makarantun suke iya shafa. Kenan yara 900 aka karantar a cikin shekara.

‘’Adiflor’’ ta kawo gudunmuwar ƙamusoshi saboda malamai, da kuma wasu littattafan koyarwa.

Tun 2011

Bugu da ƙari, an ci gaba da gine-ginen wuraren 30 tare da haɗin gwiwar Stromme Foundation, azuzuwa 30 aka bude a watan Janairu 2012 a yankin Zinder (10 kwamun ta Guidimuni, 10 a cikin kwamun ɗin Gure da 10 a kwamun ɗin Kelle). Gwamnatin Nijar ta ɗaura wa RAEDD nauyin aiwatar da aikin nan.

Daga shekara ta 2011 zuwa 2016, RAEDD ta kafa ɗakunan karatu 255 a yankunan Nijar da dama tare da goyon bayan gwamnatin, da UNICEF da gungiya mai zamen kanta Save Children. Fiye da yara 7600, a cikinsu kashi na mata 50 cikin dari suka yi amfani da tsarin. Taimakon gungiyar Stromme ya tsaya a 2013 amma aikin yana ta ci gaba.

A cikin 2018-2019, RAEDD ta kafa azuzuwan gaggawa 20 (10 a cikin sashen Maine-Soara da 10 a yankin Diffa) tare da tallafin jihar Nijer.

Ba a sabunta aikin ba tun karshen shekarar 2019.

Photo d’Alain Roux