Dandalin Kungiyoyin Hadin Kan Kasashen Duniya sakamakon Hijira (FORIM) dandamali ne na ƙasa wanda ya haɗu da ƙungiyoyi sama da 1000 na cibiyoyin sadarwa, da na Ƙungiyoyin Kawancen Kasashen Duniya sakamakon Hijira (OSIM), suna yin ayyukan haɗin kai a nan da ayyukan ci gaba a cikin kasashen da suka fito a yankin kudu da hamadar Sahara, Maghreb, Asiya ta kudu maso gabas, Caribbean da tekun Indiya.
FORIM na sa hannu game da bayar da tallafin kudi ga shirin AECIN “Tsaftar Daliban Makarantar Sakandare, Ci gaba da Karatun ’Yan Mata da Yaki da yin Aure da wuri” tare da gina salangogi a kwalejoji, lamarin da ke ba da fifiko ga kula da yara mata masu zuwa makaranta.