Tun watan janairu 2015, abokan Nijar ba su cikin ƙungiyar sadawar Tarbiyya Tatali

Don samun karin bayani kuna iya zuwa akan sabon yanar zanar su website.

Ƙungiyar ‘’Les Amis du Niger’’, an kafa ta a cikin watan nobamba ta 2001, kuma tana da cibiyarta a garin Janzé mai nisan kilometir 25 da birnin Rennes na ƙasar Faransa. Gurinta shi ne na girka dangantaka tsakanin kwaminonin Ille-et-vilaine da wasu garuruwan ƙasar Nijar. Da farko dai, ƙungiyar ta taimaka wajen ci-gaban garin Goru kirai wanda yake kusan birnin Yamai, da Anguwal saulo da ke kusan Dogon Dutsi, ta hanyar ɗaukar magoya-bayanta a Janzé da le petit Fougeray. San nan, daga amini zuwa amini, kaɗan kaɗan sai ta yi suna a cikin ƙasar Faransa. A shekara ta 2004, sai garin Gofat da ke kusan Agadas ya ƙaru, ya zama gari na uku (3) kenan. A shekara ta 2008, ƙungiyar ta ƙumshi kimanin magoya baya 100 masu yin zubin kuɗi.

A cikin niyyarta ta inganta makarantun boko da kyautata kiwon lafiya, ƙungiyar ta duhuma cikin tsarin samar wa
Kowane d’an makaranta na da littafi na kowane fanni. Ta gina ajin makaranta a garin Goru kirai da Anguwal saulo, kuma ta ɗauki nauyin albashin malaman biyu (2).

Bayan haka, ta bunƙasa wasu ayyuka daban da na makarantun ta hanyar sayar wa kowane ɗan makaranta ɗan akuya guda, domin ya kiwata shi ya ƙosar da shi, san nan ya sayar da shi bayan ƴan watanni. Ana raba ribar da aka samu tsakanin ɗan makarantar da kwamitin mai kula da tsarin. Hakan yana ƙara yawaita yaran kaɗan kaɗan.
A fannin kiwon lafiya kuwa, ƙungiyar ta gina ɗakunan shan magani biyu a Anguwal Saulo da Gofat, kuma ta ɗauki nauyin horon malam likitan da albashinsu.
A Anguwal Saulo da Gofat, ta kafa bankin cimaka, kuma ta gina rijiyar siminti a Anguwal Saulo. Domin waye kan magoya bayanta da al’umma a game da al’adun ƙasar Nijar da matsalolin da ƙasar ta fuskanta, ƙungiyar tana tsara bikin nunin abubuwan ƙasar, har a cikin ƙananan makarantun boko da na ‘’kwaleji’’ idan suka yi buƙata.

Kuɗin gudanar da ayyukan

Kuɗin kanta ne ƙungiyar ‘’Les Amis du Niger’’ take sakawa domin zartar da ayyukanta. Kuɗin sun fito daga waɗannan hanyoyin :

  • Tarbacen kuɗi daga mambobinta ;
  • Saide-saiden kayan aikin hannu na Nijar ;
  • Saide-saiden huren ado da magoya bayanta suke nomawa ;
  • Taimakon da ƴan makaranta sukan kawo, ko wasu mutane daban…
  • Tallafin da barikin ‘’Janzé’’ da le ‘’petit Fougeray’’ suke badawa.

 

Archives