An kammala wannan mataki.

Ta hanyar hulɗa tsakanin Tarbiyya Tatali da ‘’Aide et Action’’, ɗakunan littattafai 22 aka yi a cikin jahar Dogon Dutsi.

Raba ma gururuwa akwatunan littattafai.

Wannan tsarin ya biyo bayan tsarin samar ma kowane ɗan makaranta littafi ɗaya na kowane fannin karantu, wanda ya sanya ake samun littafi har a gida, dangance da littattafan gatana don yin alaƙa tsakanin al’adun gida da abin da ake koyo a makaranta.

Akwatunan littattafan da aka raba wa garuruwa sun ƙunshi littattafai na Faransanci da na hausa ; akwai littattafan ƙagaggen labari da na gatanai, akwai na fusa’o’i, akwai ƙamusoshi. A farkon shekarar 2009, ‘’Adifflor’’ ta ba da littattafai da yawa don ƙarfafa ɗakunan littattafan.

Photo d’Alain Roux